logo

HAUSA

Kasar Sin na zamanintar da tsarin gudanar da mulkin kasa da karfinta a fannin bin doka

2020-11-18 20:10:41 CRI

Kasar Sin na zamanintar da tsarin gudanar da mulkin kasa da karfinta a fannin bin doka

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada a wajen wani taron aiki kan gudanar da mulki bisa doka a dukkan fannoni, wanda aka shirya a kwanan baya a nan birnin Beijing cewa, ya kamata a dage kan zamanintar da tsarin gudanar da mulki da karfinta a fannin bin doka, da kuma nacewa kan inganta dokokin cikin gida, da kuma dokokin da suka shafi kasashen waje baki daya.

A ko da yaushe, jam'iyyar kwaminis ta Sin tana ba da muhimmanci sosai ga ayyukan gudanar da dokoki, musamman fannin hade aikin raya dokoki da na hakikanin yanayin da kasar ke ciki. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tsayawa karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, shi ne babban garambawul na ciyar da ayyukan gudanar da mulki bisa doka gaba.

Kasar Sin na zamanintar da tsarin gudanar da mulkin kasa da karfinta a fannin bin doka

Ya ce babban burin inganta gudanar da mulki bisa doka a dukkan fannoni, shi ne kiyaye hakkoki da muradun al'ummomin kasar bisa doka. A yayin wannan taron, Xi Jinping ya sake gabatar da cewa, ya zama dole a mayar da martani sosai ga sabbin bukatu da fatan na jama’a, da nazarta, da tsarawa da kuma warware manyan matsalolin da jama’a suka nuna a fannin dokoki, kana da ci gaba da bunkasa tunanin mutane na yin farin ciki, da kwanciyar hankali, da nufin ba da tabbaci ga jama’a wajen zaman rayuwa, da yin aiki cikin lumana, da gamsuwa ta hanyar amfani da dokoki.

Xi Jinping ya kuma bayyana cewa, kamata ya yi a inganta kafa dokoki a fannoni masu muhimmanci kamar tsaron kasa, da kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, da kiwon lafiyar jama'a, da tsaron halittu, da kare muhalli, da rigakafin hadari, da dokokin da suka shafi kasashen waje, da kuma tabbatar da ci gaban sabbin sana’o’i yadda ya kamata, ta hanyar bin dokokin da suka dace da kyakkyawan shugabanci. (Bilkisu Xin)