logo

HAUSA

Fasahohin zamani su ne tushen ci gaban kasa

2020-11-18 17:29:37 CRI

Fasahohin zamani su ne tushen ci gaban kasa

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne birnin Shenzhen ya cika shekaru 40 da zama yankin tattalin arziki na musamman. Birnin Shenzhen ya zama wani bangare dake bayyana ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen ketare. Yana kuma daga cikin yankunan musamman na farko-farko da kasar Sin ta kafa. Kusan shekaru 40 da suka gabata, Shenzhen ya kafa muhimmin tarihi na bunkasa daga wani karamin kauyen kamun kifi dake kan iyaka, zuwa birni mai matukar tasiri a mataki na kasa da kasa.

Tun ba a je ko’ina ba, birnin ya sake shirya bikin baje kolin manyan fasahohin zamani karo na 22 (CHTF) inda aka baje kolin sabbin na’urori 1,790 gami da sabbin fasahohin zamani 767. Abin da ke nuna cewa, fasahohin zamani na iya zama tushen ci gaban kasa, kuma idan aka naura niyya babu abin da ba za a cimmawa ba.

Taken bikin na bana wanda mahalartar sama da 3,300 daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 53 suka halarta ta kafar bidiyo da kuma ido da ido, shi ne “Farfado da makomar fasahohin kere-kere da samun bunkasa ta hanyar kirkire-kirkire.”

An kuma baje kolin manyan ayyukan fasahohi na zamani sama dubu 9, ciki har da fasahar sadarwa ta 5G, da kwaikwayon tunanin dan-Adam, da na’urorin zamani da ake amfani da su a masana’antu, da motoci masu sarrafa kansu, da rumbun bayanai, da samar da hidimar bayanai. Haka kuma, bikin na kwanaki biyar, ya samu kimanin mutane 451,000 da suka kalli kayayyakin da aka baje kolinsu.

An dai fara shirya bikin ne, a shekarar 1990, kuma yana daya daga cikin manyan bukukuwan baje kolin fasahohi na zamani mafiya girma da farin jini a kasar Sin

A yayin da birnin Shenzhen ke ci gaba da bude kofarsa ga kowa. Ita ma kasar Sin tana maraba da karin kasashe da su shiga a dama da su cikin manufarta ta yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare, da raya yankunanta na musamman na tattalin arziki, domin samar da wani sabon tsarin zurfafa tuntubar juna, da hada kai wajen ba da gudummawa da samun moriya tare. (Ibrahim Yaya)