logo

HAUSA

Hadin kai ne kadai hanya daya tilo ta raya moriyar Sin da Amurka

2020-11-17 17:06:11 CRI

Hadin kai ne kadai hanya daya tilo ta raya moriyar Sin da Amurka

Wasu rahotanni na bayyana cewa shugaban Amurka Donald Trump, na shirin kakabawa Sin wasu karin takunkumi a wannan yanayi da duniya ke matukar bukatar zama tsintsiya daya madaurinki daya. Kasashen Sin da Amurka su kasance manyan kasashe a duniya ta fuskar ci gaba da arziki da kuma fada a ji. Bisa wannan matsayin da suka taka, kamata ya yi a ce har kullum sun kasance abun koyi ga kasashe masu tasowa. Kamar yadda a kullum kasar Sin ke bayyanawa, kasashen biyu da jama’arsu za su fi amfana daga hadin gwiwa da kyautata dangantakarsu maimakon akasin hakan.

Da yake tsokaci game da wannan sabon rahoto, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhoa Lijian, ya ce har kullum, Sin na fatan inganta hadin gwiwa da Amurka, kasancewar hakan ne kadai zai amfani sassan biyu, haka zalika, shi ne hanya daya da ta rage musu.

Kamata ya yi a ce bangaren Amurka ya dauki darasi daga yadda ya tsunduma tare da raunata dangantakar dake tsakaninsa da Sin. Bisa la’akari da cewa, tun bayan kaddamar da yakin cinikayya a tsakaninsu, babu wani alfanu da hakan ya haifar, illa kara matsi a kan kamfanoni da al’ummominsu. Duk abun da hakuri da fahimta da adalci ba su kawo ba, kishiyoyinsu ba za su kawo ba. Wato babu abun da fito-na-fito tsakanin bangarorin biyu zai haifar face karin lahani ga moriya da muradunsu.

Ban da haka, har yanzu wasu jami’an Amurka na ci gaba da takalar kasar Sin ta hanyar keta manufar “Kasar Sin Daya Tak a Duniya”. Duk da cewa a ranar Asabar, wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya ce kasar tana kiyaye cikakken iko da ’yancin kasar Sin daya tak a duniya,  hakan ya saba da furuci ko ayyukan wasu jami’an gwamnatin kasar. Bai kamata a ce ana samun irin wannan daga wajen babbar kasa kamar Amurka ba. Muddun ana neman tabbatar da zaman lafiya da adalci da mutunta juna a duniya, to dole ne a rika kiyaye ka’idojin hulda da muradun kasa da kasa.

Kasar Sin ta sha bayyana cewa, ba za ta yi kasa a gwiwa wajen kare muradu da tsaronta ba, haka kuma duk wani yunkuri na yi wa wadannan muradu na ta zangon kasa, zai fuskanci martanin da ya dace da shi. Hausawa sun ce zaman lafiya, ya fi zama dan sarki, don haka, ya kamata Amurka ta yi karatun ta nutsu ta kuma kujewa zama babbar kwabo, ta gane cewa, takalar fada ba za ta haifar da da mai ido ba. Hadin gwiwa bisa zaman lafiya da adalci da girmamawa da mutunta juna, ita ce kadai mafita ga Sin da Amurka, kuma wannan mataki ba su kadai da jama’arsu zai amfanawa ba, har ma da daukacin al’ummun duniya. (Faeza Mustapha)