logo

HAUSA

Me ya sa duniya take mamakin ganin habakar tattalin arzikin kasar Sin sama da hasashen da aka yi?

2020-11-17 21:32:39 CRI

Me ya sa duniya take mamakin ganin habakar tattalin arzikin kasar Sin sama da hasashen da aka yi?

Kwanan nan, kasar Sin ta fitar da alkaluman kididdigar da ta yi kan tattalin arzikinta a watan Oktobar bana, inda kamfanin dillancin labaran Bloomberg News ya ce, tattalin arzikin kasar Sin ya samu saurin farfadowa a watan Oktoba, al’amarin da ya nuna cewa, akwai yiwuwar a bana, kasar za ta kasance kasa daya tilo wadda za ta samu habakar tattalin arziki a cikin wasu muhimman kasashe masu karfin tattalin arziki a duk fadin duniya.

Haka kuma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a watan Oktobar bana, ya zarta hasashen da aka yi.

Me ya sa duniya take mamakin ganin habakar tattalin arzikin kasar Sin sama da hasashen da aka yi?

A halin yanzu, kasar Sin tana samun babban ci gaban masana’antu, a yayin da kuma harkokin saye da sayarwa, gami da ayyukan zuba jari ke dada farfadowa. Ban da haka, harkokin neman guraban ayyukan yi da zaman rayuwar al’umma, duk suna ta bunkasa yadda ya kamata a kasar ta Sin.

A karshen watan Oktoba, shahararriyar cibiyar nazarin kasuwannin kasa da kasa mai suna IHS Markit, ta gudanar da wani bincike kan kamfanoni sama da 6600 dake kasashe 12, inda sakamakon binciken ya shaida cewa, ayyukansu a kasar Sin sun fi samun farfadowa cikin sauri. Rahoton da cibiyar IHS Markit ta bullo da shi ya bayyana cewa, dimbin damammakin saye da sayarwar da kasar Sin take bayarwa, suna kara fadada muhimmancin kasar a duk fadin duniya, a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki.

A watannin da suka wuce, ana kara fahimtar yadda kasar Sin take da babban karfi na raya tattalin aziki, da kuma kyakkyawar makoma. Sakamakon karin manufofin da ake aiwatarwa, kasar za ta kara samun ci gaban tattalin arziki, har ma ta kammala burin da aka tsara na bana, al’amarin da zai karfafa imanin duniya, kan farfadowar tattalin arziki.  (Murtala Zhang)