logo

HAUSA

Don me shugaba Xi Jinping ya kai ziyara yankunan Shenzhen da Pudong cikin wata daya?

2020-11-13 20:52:07 CRI

Don me shugaba Xi Jinping ya kai ziyara yankunan Shenzhen da Pudong cikin wata daya?

A cikin wata guda, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci birnin Shenzhen da yankin Pudong na Shanghai don halartar bukukuwan murnar cika gomman shekaru na kafuwarsu a matsayin yankunnan musamman na raya tattalin arziki, tare kuma da tsara muhimman shirye-shirye kara ci gabansu. Matakin da ya bayyana kara yin kwaskwarima a gida a bude kofa ga waje da kuma yin kirkire-kirkire da Sin ta dade tana yi. Ta wadannan tagogi biyu, ba ma kawai duniya tana iya gano niyyar kasar Sin ta yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje a sabon mataki ba, har ma ana iya fahimtar manyan damammakin da Sin take samarwa da ma ganewa idanunsu kuzarin manufofin kasar Sin.

Bisa shawarwarin da aka gabatar game da shirin raya tattalin arziki da jin dadin jama’a na shekaru biyar-biyar karo na 14 a kwanan baya, wani sabon muhimman mataki ne na zamanintar da kasar ta zamani mai bin tsarin gurguzu a duk fannoni, ta hanyar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje da kuma yin kirkire-kirkire. Wadannan matakai uku ba kawai sun zama dalilin da ya sa Shenzhen da Pudong sun samu bunkasuwa cikin sauri ba, har ma sun zama tushen samun sabon bunkasuwa ta dogaro da kansu da zama abin misali ga sauran wurare a fannin samun ci gaba na zamani.

Sabon muradun samun bunkasuwa na wadannan wurare biyu ba kawai yana nuna matakan da Sin take dauka a fannin yin kwaskwarima da bude kofa kawai ba, yana kuma bayyanawa duniya alkawari da kuma niyyar kasar Sin na yin kwaskwarima da ci gaba da kara bude kofa.

Bude kofa da samun bunkasuwa tare, ita ce manufar kasar Sin, wadda ta bayyana burin kasar da ma nauyin dake wuyanta na ingiza gina tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa da raya kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya.

An yi imanin cewa, wadannan wurare biyu za su samu bunkasuwa na al’ajabi da duniya za ta nuna sha’awarsa, da samar da sabbin damammaki ga duniya, za kuma su kara bayyana kuzari da ci gaban tsarin mulkin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin. (Amina Xu)