logo

HAUSA

Jam’iyyar Kwaminis Mai Mulkin Sin Ta Cancanci Yabo

2020-11-12 17:17:47 CRI

Jam’iyyar Kwaminis Mai Mulkin Sin Ta Cancanci Yabo

A baya bayan nan, JKS ta shiga bakin wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya, da wasu ’yan siyasar Amurka, wadanda suka yi ta kokarin shafa mata kashin kaji ta hanyoyi daban daban. To amma gaskiyar al’amari shi ne, JKS ita ce ginshikin ci gaban kasar Sin, a bangarorin raya tattalin arziki da zamantakewa, irin ci gaban da ya zamewa duniya gagara badau, kuma mai cike da ban mamaki.

Ko shakka babu, JKS ta sha banban da sauran jam’iyyun siyasa, duba da yadda tun kafuwarta a watan Yulin shekarar 1921, ta cimma nasarar kafa salon mulkin gurguzu mai halayyar musamman na Sin. Kaza lika jam’iyyar ta yi nasarar ganin an kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949. Kuma duk da cewa an fara aiwatar da sauye sauye a tsarin kasuwar kasar Sin tun daga karshen shekarun 1970, jami’iyyar ta tabbatar da dorewar kasar kan tsarin kwaminisanci, daidai da bukata da yanayin da kasar ke ciki.

JKS na daf da cika shekaru 100 da kafuwa, a kuma wannan gaba, tana ci gaba da aiki tukuru wajen fadada ci gaban tattalin arziki, da sanya kasar Sin a sahun gaba ta fuskar karfin fada a ji, duk kuwa da kalubalolin da kasar ke fuskanta daga abokan takara, da ma yadda cutar COVID-19 ya mayar da hannu agogo baya a sassa masu yawa.

Bugu da kari, kyawawan manufofin JKS, da kwazon aiki na al’ummar Sinawa, sun taka rawar gani wajen cimma nasarorin da kasar ta samu. Karkashin kudurorin ci gaba na shekaru biyar da Sin din ke aiwatarwa da taimakon JKS tun daga shekarar 1953, yanzu haka a shekara mai zuwa ne, kasar za ta kai ga zango na 14 karkashin wannan tsari.

Salon JKS game da aiwatar da shawarwari, ya dace da tsarin dimokaradiyya. Wanda karkashinsa, kasar ta kai ga nasarar ciyar da al’ummunta da yawansu ya kai biliyan 1.4. Baya ga hakan, yanayin zaman rayuwar Sinawa shi ma ya inganta.

Muna ma iya cewa, JKS ce kashin bayan bunkasar zamantakewa, da tattalin arziki, da tsarin siyasar kasar Sin, don haka ta cancanci yabo maimakon ganin baike.

A karshe, karkashin jagorancin JKS, kasar Sin na kiran sauran sassan duniya, da su yi hadin gwiwar samar da daidaiton ci gaba, da hadin gwiwar cimma moriyar juna, da adalci a harkokin gudanarwar kasa da kasa, tare da samar da kyakkyawan yanayin muhalli mai dorewa.

Ga duk mai kallon al’amura da idon basira, zai yarda da cewa, jam’iyyar da ta cimma wadannan nasarori, tabbas ta cancanci a jinjina mata!!!! (Saminu Hassan)

Saminu