logo

HAUSA

Yadda Bikin CIIE Ke Samar Da Dimbin Damammaki Ya Sa Ake Fahimtar Muhimmancin Sin

2020-11-10 22:03:16 CRI

 

Yadda Bikin CIIE Ke Samar Da Dimbin Damammaki Ya Sa Ake Fahimtar Muhimmancin Sin

A yau Talata aka rufe bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwannin kasar Sin (CIIE) karo na 3, tare da samar da wani sakamako mai armashi, inda darajar kwagilolin da aka kulla a wajen bikin ta kai dalar Amurka biliyan 72.62, jimillar da ta karu da kashi 2.1% bisa na bikin bara. Hakan ya shaida cewa bikin CIIE ya zama wani fitaccen dandali da ke samar da damammaki na kasuwanci ga kasashe daban daban, tare da taimakawa kamfanoninsu farfadowa daga illar annobar COVID-19.

An labarta wani dan kasuwa da ya makara wajen halartar bikin CIIE sosai a kwanakin nan, Arai Mikio, wani dan kasuwan kasar Japan mai sayar da butar shayi, wanda aka yiwa gwajin kwayoyin cutar COVID-19 sau 3, tare da killace shi na kwanaki 14, a karshe ya shiga wurin da ake gudanar da bikin CIIE kwana daya kafin rufe bikin. A cewarsa, bikin CIIE wata muhimmiyar dama ce da bai kamata a kaurace ta ba. Hakika, 'yan kasuwan kasashe daban daban masu sha'awar bikin CIIE, kamar mista Arai Mikio, suna da yawa. A cikinsu, yawan kamfanoni daga kasar Amurka ya kai matsayi na 3 cikin kamfanoni na kasashe daban daban, kana sun baje kolin nau'ikan kayayyaki masu yawa. Wannan batu ya sabawa shawarar da wasu 'yan siyasan kasar Amurka ke kokarin yadawa ta neman katse huldar ciniki dake tsakanin kasar Amurka da kasar Sin. Dalilin da ya sa bikin CIIE ke samun karbuwa sosai, shi ne domin ba wanda zai dakile tsarin tattalin arzikin duniya ba. Kasar Sin tana samar da wasu manyan kasuwanni, inda jama'ar kasar suka nuna cikakken karfi wajen sayen kayayyaki na kasashe daban daban. Ban da wannan kuma kasar na ci gaba da kokarin kirkiro sabbin fasahohi, da bude kofarta ga sauran kasashe.

Wani ra'ayi na bai daya na 'yan kasuwan kasashe daban daban, shi ne sabon tsarin raya kasa da kasar Sin ta bullo da shi, ya nuna niyyar kasar ta taimakawa farfado da tattalin arzikin duniya, tare da samar da dimbin damammaki ga kasashe daban daban, domin su ma su bunkasa tattalin arzikinsu. (Bello Wang)