logo

HAUSA

Kawancen gargajiya dake tsakanin Sin da Afirka zai karu sakamakon hadin kansu wajen yaki da COVID-19

2020-11-07 16:31:42 CRI

Kawancen gargajiya dake tsakanin Sin da Afirka zai karu sakamakon hadin kansu wajen yaki da COVID-19

A 'yan kwanakin da suka gabata, ta hanyar kungiyar hadin gwiwar matan shugabannin kasashen Afirka, gwamnatin kasar Sin ta yi nasarar bayar da gudummawar kayayyakin kiwon lafiya ga mata, yara da matasa na kasashen Afirka 53 don yaki da annobar numfashi ta COVID-19. A cikin watanni hudu kawai, kasar Sin ta shawo kan matsaloli daban daban, ciki har da sufurin kasa da kasa sakamakon halin da ake ciki na yakar annoba, ta tura dukkan kayayyakin zuwa kasashen Afirka. Gwamnatocin kasashe daban daban na nahiyar Afirka sun dora muhimmanci sosai kan aikin tallafin na wannan karo, har ma wasu shugabannin kasashen da abin ya shafa, da matansu, da manyan jami'ai sun halarci bikin mika kayayyakin bi da bi, sun kuma rarraba kayayyakin akan lokaci don a yi amfani da su tun da wuri, kana kuma sun aike da wasiku don nuna matukar godiyarsu ga gwamnatin kasar Sin. Tun bayan barkewar annobar, kasar Sin da kasashen Afirka suna ta tallafawa juna tare da shawo kan matsalolin tare. Yayin da take fuskantar matsin lamba na yaki da cutar, kasar Sin ta samar da kayayyaki masu yawa na yaki da cutar cikin gaggawa ga kungiyar Tarayyar Afirka da ma kasashen Afirka ta hanyoyi daban-daban a kan lokaci, ta kuma gudanar da tarurrukan bidiyo na kwararrun masu yaki da annobar har sau 6 tare da bangaren Afirka don musayar fasahohin da ta samu wajen yaki da cutar, kana ta aika da tawagogin kwararrun likitoci na yaki da annobar zuwa kasashen Afirka 15. Kuma kungiyoyin likitocin ba da agaji 46 na kasar Sin dake nahiyar Afirka suna himmantuwa wajen shiga ayyukan yaki da cutar a wuraren. Baya ga haka kuma, kasar Sin ta yi alkawarin cewa, bayan an kammala aikin nazarin allurar rigakafin cutar da kuma amfani da ita, da farko da za a yi amfani da su a kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka. Darakta-Janar na kungiyar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a kwanan nan ya bayyana yayin wata tattaunawa cewa, yawan sabbin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afirka yana raguwa, kuma an bayyana gagarumin hasashe kan halin da ake ciki yanzu na rigakafi da shawo kan annobar. Tattaunawar ta yi imanin cewa ingantaccen aiki na ganowa, kariya da ikon kulawa a cikin ƙasashen Afirka muhimmin ne wajen yaƙar cutar. Daraktan cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Afirka, Ken Gesong, ya yi magana sosai game da magunguna da tallafin mutane daga Sin da sauran ƙasashe. Ya yi imanin cewa a ƙarƙashin jagorancin kungiyar Tarayyar Afirka da Cibiyoyin Kula da Rigakafin Cututtuka na Afirka, ƙasashe cikin hanzari kuma gaba ɗaya suka ƙaddamar da ayyuka don magance annobar kuma sun ƙaddamar da wani dandalin sayen kayan haɗin magunguna don gwamnatocin Afirka su sami kayan kariya da sauran kayan kiwon lafiya a cikin lokaci. Game da haka, daraktan cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Afirka, ya yaba sosai kan tallafin da kasashen Afirka suka samu daga kasar Sin da sauran kasashe a fannonin kayayyakin aikin jinya da kwararru.

Cutar ba ta san kasa ba, mun yi imanin cewa, bisa karfafa hadin kai bangarorin Sin da Afirka za su cimma nasarar yakar cutar, kuma tabbas kawancen gargajiya dake tsakaninsu zai karu a yayin da suke tinkarar annobar tare. (Bilkisu Xin)