logo

HAUSA

Shirin adawa da Sin da Pompeo ke gudanarwa a Asiya ya kasance abun dariya

2020-11-03 20:21:36 CRI

Shirin adawa da Sin da Pompeo ke gudanarwa a Asiya ya kasance abun dariya

A kwanan baya shugaban kasar Sri Lanka Gotabhaya Rajapaksa, ya bayyana yayin da yake zantawa da manema labarai cewa, ba zai yiwu kasarsa ta daddale yarjejeniyar tallafi ta kamfanin Millennium Challenge Corporation da kasar Amurka ba, a don haka, yunkurin adawa da kasar Sin na sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bi ruwa.

Hakika Pompeo ya gamu da matsala yayin da yake ziyara a kasashen Asiya guda biyar a kwanan baya, shirin yin adawa da kasar Sin da wasu 'yan siyasar Amurka suka tsara kafin babban zaben kasar Amurka ya kasance abun dariya. Duk da cewa, kafin babban zaben kasar Amurka, ya kamata manyan 'yan diplomasiyya su dakatar kai ziyara a kasashen waje, amma Pompeo ya je wasu kasashen Asiya domin lalata huldar dake tsakaninsu da kasar Sin. Amma ya gamu da matsala. Alal misali, yayin da Pompeo da ministan tsaron Amurka Mark Tomas Esper suka kai ziyara a kasar Indiya, sun yi shawarwari da takwaransu na kasar wato ministan wajen Indiya S Jaishankar, da ministan tsaron Indiya Rajnath Singh, domin nuna wa kasa da kasa kasashen biyu wato Amurka da Indiya suna gudanar da huldar sada zumunta dake tsakaninsu yadda ya kamata, amma bisa labarin da mujallar U.S. News & World Report ta gabatar, an ce, ainihin makasudin tattaunawar dake tsakaninsu shi ne, sayar da jirgin sama maras matuki samfurin MQ-9 ga Indiya, amma Indiya ba ta amince ba. Da haka an lura cewa, yunkurin Pompeo na neman samun goyon baya daga wadannan kasashen Asiya ya ci tura.

A halin yanzu annobar cutar COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a sassan duniya, tattalin arzikin duniya shi ma ya gamu da matsala, kusan daukacin kasashen duniya suna hada kai domin ganin bayan annobar tare, kuma da samun ci gaba. Ban da haka, kimar Pompeo a duniya ta riga ta baci, sakamakon jita-jitar da ya baza, da matakan matsa lamba da kakkaba takunkumin da ya dauka, shi ya sa babu wata kasa dake son goyon bayan Amurka ta hanyar bata moriyar kanta.(Jamila)