logo

HAUSA

Sharhi: Duk duniya Za Ta Ci Gajiya Daga Manufar Daga Matsayin Bude Kofa Ga Ketare Da Sin Ke Dauka

2020-11-01 18:56:54 CRI

A kwanan nan, an bayar da sanarwar cikakken zama na biyar na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na 19, inda aka gabatar da cewa, za a daga matsayin bude kofa ga ketare, a kokarin bude wani sabon shafin hadin kai don samun nasara tare. Sa'an nan za a bude kofar Sin a fannoni daban daban, da ma inganta hadin kai tare da kasa da kasa bisa fifikon da Sin ke da shi ta fuskar kasancewar wata babbar kasuwa don moriyar juna. Bugu da kari, za a raya sabon tsarin tattalin arzikin kasar dake dora muhimmanci kan bude kofarta, da sa kaimi ga aikin ba da sauki da 'yanci ga cinikayya da zuba jari, da kirkirar hanyar ci gaban cinikayya, a kokarin samun bunkasuwa bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", da shiga aikin kwaskwarima ga tsarin tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.

Sharhi: Duk duniya Za Ta Ci Gajiya Daga Manufar Daga Matsayin Bude Kofa Ga Ketare Da Sin Ke Dauka

Kamar yadda aka sani, bude kofa ga ketare babbar manufa ce ta kasar Sin, wadda kuma ta kasance wani muhimmin karfi na sa kaimi ga saurin ci gaban tattalin arzikinta mai dorewa. A 'yan shekarun da suka gabata, dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda ya samu cikas, kiki-kakar ciniki ma ta tsananta, wasu kasashen duniya na daukar ra'ayin ba da kariyar cinikayya da na cin gashin kai, tattalin arzikin duniya na samun tabarbarewa sakamakon bullar cutar COVID-19, duk wadannan batutuwan na damun kasashen duniya sosai ga makomar yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje daya. Amma idan mun yi hangen nesa, to zamu iya gano cewa, yadda kasa da kasa zasu hada kansu don moriyar juna da samun nasara tare hanya ce da dole ne a bi cikin dogon lokaci. Don haka, yadda kasar Sin ke ci gaba da martaba manufar bude kofa ga waje da ma kyautata matsayin manufar, zai bayar da babbar gudunmawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

Waiwaya adon tafiya. A cikin shekaru biyar da suka wuce, Sin ta fitar da jerin matakai don kara bude kofarta ga kasashen waje. Alal misali, ta amince da shigowar jarin waje a fannoni masu yawa, da gaggauta raya yankin cinikayya maras shinge, da fitar da dokar zuba jari da 'yan kasuwa baki ke yi a Sin, gami da shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo dasu kasar Sin. Duk wadannan lammuran sun shaida cewa, kasar Sin tana kokarin cika alkawarin da ta yi kan cewa, Sin ba za ta rufe kofarta ba, a maimakon haka zata kara bude kofarta ga ketare, ta yadda kasa da kasa zasu samu damammaki a fannonin kasuwanci, zuba jari da ma bunkasuwrsu.

Sharhi: Duk duniya Za Ta Ci Gajiya Daga Manufar Daga Matsayin Bude Kofa Ga Ketare Da Sin Ke Dauka

A nasa bangaren, Donald Rushambwa, manazarcin cibiyar binciken musayar tattalin arziki da al'adu ta kasar Sin da Afirka ta Zimbabwe ya nuna amincewa sosai ga wannan matakin da Sin ke dauka. Ya ce, matakin zai amfani dukkan kasashen duniya, ciki har da Zimbabwe. Daukar ra'ayin kashin kai ba daidai bane, cinikayyar duniya ba za ta samu bunkasuwa ba, sai idan an martaba ra'ayin kasancewar bangarori daban daban, tare da inganta hadin kan kasa da kasa, ta yadda za a amfanawa dukkan kasashe gaba daya. A ganinsa, yadda Sin da kasashen Afirka ke hadin kansu ta fuskar samar da muhimman ababen more rayuwa ya kasance wani abin misali, inda bangarorin biyu suke taimakawa juna a fannin masana'antu, har ma sun samu moriyar juna.

Ruwan da aka datse shi baya gudana ba rayayye ba ne, amma ruwan dake cikin kogi rayayye ne. Kasar Sin dake zamanin yanzu, ba ita kadai ba ce, tana da nasaba da kasashen Asiya, har ma da kasashen duniya. Daga shekara mai zuwa, kasar Sin zata kaddamar da wani sabon shirinta na samun ci gaba, idan ta iya kara bude kofarta don rungumar duniya, to tabbas ne zata kara bayar da sabuwar gudummawa ga ci gaban duniya, tare da samar da wata kyakkyawar makoma ga daukacin bil Adama.(Kande Gao, sashen Hausa na CRI)