logo

HAUSA

Kasar Sin ce mafi karfin kirkire-kirkire da inganta ci gaban duniya

2020-10-31 22:01:14 CRI

Kasar Sin ce mafi karfin kirkire-kirkire da inganta ci gaban duniya

 

"Kasar Sin ta yi alkawarin tsayawa kan neman ci gaba mai inganci da kuma raya kimiyya da fasaha a cikin shirinta na shekaru 5", "Sabon shirin na shekaru biyar na kasar Sin yana da burin gina wata babbar kasa mai karfin fasahohi a duniya." A cikin kwanakin nan da suka gabata, kafofin watsa labarai na duniya kamar Bloomberg da mujallar Fortune sun ciro kalmar "kirkire-kirkire" daga sanarwar da aka bayar a cikakken zaman taro na biyar na kwamitin tsakiya na 19 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin. Kamar yadda suka dora muhimmanci a kai, "Shirin na shekaru biyar na 14" da aka zartas, ya gabatar da shawarar dagewa kan ainihin matsayin kirkire-kirkire a yayin da ake kokarin zamanantar da kasar Sin gaba daya, da mayar da dogaro da kai a fannin kimiyya da fasaha matsayin ginshikin bunkasa kasa, haka kuma, ya zama jigon ayyuka daban-daban. Wannan shi ne karo na farko da aka tabbatar da hakan a tarihin JKS na samar da shirin ci gaba na shekaru biyar, wanda ke nuna muhimmancin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha a yunkurin ci gaban kasar Sin a nan gaba.

 

Kasar Sin ce mafi karfin kirkire-kirkire da inganta ci gaban duniya

 

Duba da yadda a ko da yaushe masu tsara manufofi na JKS ke mayar da bukatun jama'ar kasar na neman ingantaciyyar rayuwa a matsayin tushen karfafa kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da nacewa ga yin kirkire-kirkire domin biyan bukatar kasuwa, kasar Sin ta samu ci gaba mai inganci sosai yayin shirin shekaru 5 karo na 13. Kamfanin Deloitte ya yi hasashe a cikin rahotonsa mai taken "Nazari da tunani kan masana'antu na shirin shekaru biyar karo na 14", cewa a lokacin" Shirin shekaru biyar na 14 ", ana sa ran fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta kasar Sin da karfin amfanin fasahar za su kai matsayi daya da na duniya, fasahar kuma za ta zama wani sabon muhimmin abu na bunkasar tattalin arziki.

 

Kasar Sin ce mafi karfin kirkire-kirkire da inganta ci gaban duniya

 

"Jagorantar fannin kimiyya da fasaha na duniya, da fuskantar babban filin yaki na bunkasar tattalin arziki, da fuskantar manyan bukatun kasar, da fuskantar rayuwar jama'a da lafiyarsu", shi ne burin da kasar Sin za ta yi kokarin cimmawa ta hanyar kirkire-kirkire a lokacin da bayan shirin na shekaru 5 na 14. Bisa wannan jagoranci, Sinawa masu ra'ayin kirkire-kirkire za su ci gaba da bude sabon babin neman ci gaba, da tsara sabbin fa'idodin ci gaba, a lokaci guda kuma suna fadada hadin gwiwa a fannonin kimiyya da fasaha, tare da hada karfi cikin tsarin kirkire-kirkire na duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)