logo

HAUSA

Shigar da matasa cikin manufofin dandalin FOCAC na da makoma mai haske ga dangantakar Sin da Afrika

2020-10-27 16:44:54 CRI

Shigar da matasa cikin manufofin dandalin FOCAC na da makoma mai haske ga dangantakar Sin da Afrika

A jiya Litinin ne aka kaddamar da bikin matasan Sin da Afrika karo na 5 a nan birnin Beijing, domin murnar cikar dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC shekaru 20 da kafuwa. Dandalin FOCAC da aka kafa shekaru 20 da suka gabata, dandali ne da ya samar da kafar kyautata hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika, inda ya amfanawa nahiyar Afrika a fannoni da dama ta yadda ya kai ta ga samun ci gaban tattalin arziki da cinikayya da kayayyakin more rayuwa da tallafi a fannoni da dama. Duk da cewa dandalin ya kunshi bangarori da dama, batun musaya da kyautata mu'amala tsakanin matasan bangarorin biyu, daya ne daga cikin bangarorin da dandalin ya mayar da hankali a kansu. A ko da yaushe, kasar Sin kan yi hangen nesa, ta kuma lalubo dabarun da za su dore tare da samar da alfanu a nan gaba. Kuma batun kyautata mu'amala da musaya tsakanin matasan bangarorin biyu, abu ne mai matukar muhimmanci da za a ga amfaninsa a nan gaba, ko da ba a gani ba a yanzu.

Shigar da matasa cikin manufofin dandalin FOCAC na da makoma mai haske ga dangantakar Sin da Afrika

Yayin da ake fama da matsaloli da dama a duniya, kama daga tattalin arziki zuwa tsaro da kiwon lafiya, kasashe ba su cika bada wani fifiko ga abubuwan da za su bunkasa ci gaban matasa ba, haka kuma sun gaza gano ainihin muhimmancin da matasan ke da shi ga ci gaban kasashensu a yanzu da kuma nan gaba. Haka zalika, sun gaza gano cewa, idan ba a ba su damarmaki tare da horar da su ba, matasan na iya karawa matsalolin da ake fuskanta kamari. Kamata ya yi, duk wata dabara ko hadin gwiwa ko manufa ta rika yin hangen nesa, ta yadda za ta hango irin gudunmawar da matasan za su iya bayarwa ga ci gaban kasa da kasa da ma duniya baki daya.

Kasar Sin ta yi matukar dabara bisa bullo da wannan shiri, da a bana ya shiga shekara na 5 da fara kaddamarwa. Yayin bikin na bana, wanda zai shafe kwanaki 7, wakilan matasan Afrika 42, za su ziyarci masana'antu da cibiyoyin fasahohin zamani dake Beijing da lardin Jiangxi na gabashin kasar Sin, kana za su tattauna da wakilan matasan kasar Sin. Wannnan zai kara fahimtar da su ci gaban kasar Sin da kuma kara fahimtar yanayin al'ummarta.

A wannan zamani da ake ciki, matasa suna da gaggarumar rawar taka wajen kawo sauye-sauyen a duniya domin ci gabanta. Alkaluman da AU sun nuna cewa, sama da kaso 75 na al'ummar Afrika biliyan 1.2 'yan kasa da shekaru 35 ne. La'akari da haka, ziyarar wakilansu a kasar Sin tare da mu'amala da takwarorinsu na kasar, zai yi ta zurfafa dangantakar Sin da Afrika ta yadda za su kara dunkulewa su zama tsintsiya madaurinki daya. (Faeza Mustapha)