logo

HAUSA

Sin Tana Ba Kasashen Duniya Gudunmawa A Yaki Da Talauci

2020-10-25 16:22:59 CRI

Sin Tana Ba Kasashen Duniya Gudunmawa A Yaki Da Talauci

Dangane da yadda ake gudanar da ayyukan kawar da talauci a kasar Sin, al'ummomin kasar su kan ce, idan muka kwatanta da irin zaman rayuwarmu a da, da zaman rayuwa a halin yanzu, tamkar shan zuma ne, yana da dadi, ba mu taba yin zaton hakan ba.

Cimma nasarar kawar da talauci baki daya, shine alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta yiwa al'ummomin kasa da kasa domin gina zaman rayuwar al'umma mai matsakaciyar wadata. A bana, gwamnatin kasar Sin ta dukufa wajen yaki da cutar COVID-19, yayin da take ci gaba da aiwatar da ayyukan kawar da talauci a dukkan fadin kasar Sin baki daya. Bisa Shirin gwamnatin, ya zuwa karshen shekarar bana, mutane kimanin miliyan 100 za su fita daga kangin talauci, lamarin da ya nuna cewa, Sin za ta cimma burin kawar da talauci cikin jadawalin neman dauwamammen ci gaba na MDD zuwa shekarar 2030, wato kafin shekaru 10 da aka tsara cikin wannan jadawali. Wannan nasarar da kasar Sin za ta cimma, za ta samar da darussa masu kyau da kuma bada babbar gudummawa ga kasa da kasa a fannin yaki da talauci. A yayin da kasar Sin take dukufa wajen aiwatar da ayyukan kawar da talauci cikin gida, tana kuma ba da taimako yadda ya kamata ga kasashe masu tasowa da ma sauran kasashe marasa ci gaba, domin nuna musu goyon baya wajen raya tattalin arziki da yaki da talauci. Cikin ko da yaushe, kasar Sin tana dukufa wajen karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin kawar da talauci, domin inganta dunkulewar dukkanin bil Adama.

Bayan kawar da talauci baki daya a kasar Sin, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta ba da jagoranci da al'ummomin kasar domin gina wata kasa ta zamani a dukkan fannoni bisa tsarin gurguzu, da kuma cimma buri na samun matsakaciyar wadata. A sa'i daya kuma, Sin za ta ci gaba da ba da taimako ga kasa da kasa ta fuskar ayyukan kawar da talauci, domin kawar da talauci baki daya a duk fadin duniya da kuma neman ci gaban dukkanin bil Adama a duk fadin duniya. (Maryam Yang)