logo

HAUSA

Jama'ar Sin Masu Kishin Zaman Lafiya Ba Su Jin Tsoron Tsokanar Da Aka Ta Da

2020-10-23 21:07:00 CRI

Yau Jumma'a 23 ga wata, an yi bikin cika shekaru 70 da sojoji masu sa kai na kasar Sin suka taimaka wa Koriya ta Arewa wajen turjewa zaluncin Amurka, inda shugaba Xi Jinping ya yi wani muhimmin jawabi. A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya waiwayi wahalhalun da kasar Sin ta taba sha cikin yakin, da kuma ma'anar yakin a tarihi, ya kuma aike da sakonni na cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan kiyaye ikon mulkin kan kasa, da cikakkun yankunan kasa, tare da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da take ciki da ma duniya baki daya. Dalilin da ya sa kasar Sin ta shirya gagarumin bikin a yau shi ne, koyon darasi daga tarihi, a kokarin kara kiyaye zaman lafiya, a maimakon ci gaba da yin adawa. In an kwatanta zamanin yau da kuma shekaru 70 da suka wuce, kasashen duniya na kokarin neman zaman lafiya da ci gaba. Amma wasu 'yan siyasan Amurka ba su koyi darasi daga tarihi ba, suna cin zalin kasar Sin, a yunkurin kwace wa kasar Sin ikonta na neman samun ci gaba, tare da sake wanzar da baraka da tashin hankali a duniya. Jama'ar Sin suna kishin zaman lafiya, ba su nemi yin danniya da fadada yankunanta ba har abada, amma ba za su yarda da a illanta ikon mulkin kan kasarsu ba.

Jama'ar Sin ba su taba ta da matsala ba, amma ba sa jin tsoron kare kai idan an tada wata matsala. Ba sa jin tsoron kawo musu barazana. Ba za a tsoratar da al'ummun Sinawa wadanda ba za su mika wuya sakamakon matsin lamba ba. Jama'ar Sin suna tsayawa kan raya kasa cikin lumana, tana bude kofa ga ketare, tana kuma yin hadin gwiwa da kasashen duniya, a kokarin samun ci gaba tare. Za su hada kan jama'ar kasa da kasa wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama, a kokarin samun kyakkyawar makoma mai zaman lafiya da ci gaba. (Tasallah Yuan)