logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Cika Alkawarin Kara Azamar Ganin Kowa Ya Samu Rigakafin Cutar COVID-19 Cikin Adalci

2020-10-22 20:30:16 CRI

Kwanan baya, labarin shigar kasar Sin cikin shirin COVAX, ya jawo hankalin kafofin yada labarun duniya sosai. A matsayinta na wata kasa da ke kan gaba a duniya, a fannin nazarin alluran rigakafin cutar numfashi ta COVID-19, ana gudanar da gwajin alluran iri guda hudu kan mutane bisa mataki na uku lami lafiya a kasar, kana kuma kasar Sin za ta iya samar wa kanta isassun alluran. To ko me ya sa kasar Sin ta tsai da kudurin shiga wannan shiri da hukumar lafiya ta duniya, wanda kawancen shirin alluran rigakafin cututtuka na duniya wato GAVI suka tsara cikin hadin gwiwa? Kamar yadda gwamnatin Sin ta jaddada sau da dama a kwanan baya, dalilin da ya sa kasar Sin ta shiga shirin shi ne, kara azamar samar da alluran cikin adalci a duniya, da tabbatar da kasashe maso tasowa sun samu alluran, sa'an nan da karfafa gwiwar karin kasashen su shiga cikin shirin, su kuma goyi bayan shirin. A daidai wannan muhimmin lokacin da ake yaki da annobar, matakin da kasar Sin ta dauka ya nuna cewa, ta cika alkawarinta na sanya alluran zama kayan al'ummar duniya baki daya, da kokarin ganin kowa ya samu alluran, kowa ya iya biyan kudin alluran. Shugabar kwamitin kungiyar tarayyar Turai Madam Ursula von der Leyen, ta yi maraba da shigar kasar Sin cikin shirin COVAX, inda ta yi nuni da cewa, manufar cudanyar sassa daban daban, ta taka muhimmiyar rawa wajen cimma burin duniya, na ganin duk wanda yake bukatar allurar ya same ta a ko ina yake a duniya. Har ila yau, kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ce, shigar kasar Sin cikin shirin na COVAX ya ciyar da shi gaba sosai. Yanzu haka, yawan masu kamuwa da cutar COVID-19 ya wuce miliyan 40 a duniya. A wannan muhimmin lokaci, kasar Sin ta sauke nauyin da ke bisa wuyanta, wanda ya karfafa gwiwar kasashen duniya na yaki da annobar tare, kana kuma ya nuna cewa, kasar Sin tana kawo wa kasashen duniya zarafi, a maimakon barazana. Kuma ita abokiya ce, maimakon abokiyar gaba. (Tasallah Yuan)