logo

HAUSA

Mu gudu tare, mu tsira tare

2020-10-20 20:13:53 CRI

 

Mu gudu tare, mu tsira tare

 

Kimanin watanni 10 bayan sanar da bullarta a hukumance, har yanzu annobar COVID-19 na ci gaba da yaduwa a duniya, inda zuwa jiya Litinin, adadin wadanda suka kamu da cutar a fadin duniya, ya kai 39,944,882, sannan yawan wadanda ta yi ajalinsu ya kai 1,111,998.

Yayin wani taro ta kafar bidiyo da aka yi jiya, Darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghbreyesus, ya ce yanzu an shiga wani muhimmin lokaci na damuwa, la'akari da karatowar lokacin hunturu. A don haka, ya ce akwai bukatar gwamnatoci su mayar da hankali wajen datse dukkan hanyoyin da cutar take yaduwa, saboda kada hannun agogo ya koma baya. Ya kara da bayyana cewa, zuwa yanzu, jimilar kasashe 184, sun shiga cikin shirin COVAX da hukumarsa ke jagoranta, wanda ke da nufin samar da riga kafin cutar ga al'ummar duniya cikin adalci. A lokacin da ake fargabar kara fadawa cikin matsanancin yanayi saboda cutar, lallai ana tsananin bukatar karin hadin gwiwa da goyon baya wajen samar da riga kafin. Tuni dai wasu kasashe masu arziki suka sayi adadi mai yawa na riga kafin tun ma kafin a kammala gwaji. Son kai da bawa kai fifiko a yanzu, ba abu ne da zai haifar da da mai ido ba, la'akari da cewa, annobar nan da ta tashi bulla, ba ta yi shawara da kowa ba, haka kuma ba ta ware wata kasa ko wani launin ko addini ba. Ya kamata kasashe masu arziki dake son kansu, su nazarci yadda cutar nan ta bulla ta kuma yi mummunan tasiri ga daukacin duniya, don su gane cewa, babu bambanci tsakanin bil adama.

A baya-bayan nan ne kasar Sin ta sanar da kudurinta na shiga shirin na COVAX, lamarin da ya nuna matsayinta na babbar kasa dake taka muhimmiyar rawa kan al'amuran da suka shafi duniya. Duk da cewa tana da dimbin al'umma, kasar Sin za ta iya samar da riga kafin ga sauran kasashe, saboda masana na da yakinin cewa, ta kusan kawar da duk wata hanya ta yaduwar cutar tun ma kafin a samu rigakafin, saboda managartan matakan da ta dauka. Ban da wannan, ya bayyana kudurinta na gina al'umma mai makoma ta bai daya ga daukacin bil Adama. Har ila yau, an yi imanin kasar Sin za ta mayar da hankali wajen taimakawa kasashe masu tasowa musamman 'yan uwanta na Afrika, inda a yanzu adadin wadanda cutar ta harba ya kai 1,644,780. Tun kafin kaddamar da wannan shiri, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, bayan samar da rigakafin, kasarsa za ta samar da shi ga kasashen Afrika da sauran kasashe masu tasowa. Hakika wannan yunkuri na kasar Sin, abu ne da zai kara mata kima da daraja da aminci a idon duniya, kuma ta nuna cewa lallai ya kamata "a gudu tare a tsira tare".