logo

HAUSA

Ra'ayin mahukunta Sin ya yi daidai da na Afrika kan hadin gwiwar bangarori daban daban

2020-10-19 19:35:34 CRI

 

Ra'ayin mahukunta Sin ya yi daidai da na Afrika kan hadin gwiwar bangarori daban daban

Da alama baki ya zo daya, kuma ra'ayin bangarorin biyu ya dace da juna. Koda yake, da ma masu hikima na cewa "da abokin daka ake shan gari" a wani kaulin kuma, "hannu da yawa maganin kazamar miya". Ga dukkan masu lura da al'amurran kasa da kasa, a lokuta da dama shugabanin kasar Sin sun sha jaddada aniyar kasarsu na neman hada kan duniya da kuma kokarin samar da dawwamman cigaba da kyautata zaman rayuwar dukkan bil adama ba tare da yin la'akari da shiyya ko yankin da mutum ya fito ba. A sau da dama, shugaban kasar Xi Jinping ya sha nanata kalmar nan ta neman hadin gwiwar bangarori daban daban, wato multilateralism a Turance, musamman a lokutan da shugaban yake gabatar da jawabai a turukan kasa da kasa kuma a lokuta daban daban. Hakan kuwa, wata manufa ce ta yunkurin shugaban na kokarin hada kan al'ummar kasa da kasa domin a gudu tare a tsira tare, don kyautata makomar rayuwar dukkan 'yan Adam.

Wani abin ban sha'awa shi ne, wannan kiraye-kiraye na shugaban yana samun karbuwa da kuma goyon baya daga dukkan shiyyoyi na duniya. Nahiyar Afrika daya ne daga cikin shiyyoyin duniya da kasar Sin ke ci gaba da kulla kawance, da yin hulda ta kut-da-kut. Ra'ayin hadin gwiwar bangarori daban ya yi matukar samun gindin zama da kuma karbuwa daga shugannin kasashen nahiyar Afrika. Koda a 'yan kwanakin da suka gabata, shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU, Moussa Faki, ya bukaci a farfado da huldar bangarori daban daban a kokarin da duniya ke yi na tabbatar da ingantaccen tsarin shugabanci a duniyar. Ya ce bullar wannan annobar ta COVID-19 ta kara bayyanawa a fili cewa, dukkan 'yan Adam iyali guda ne wadanda ba za a taba raba su ba. Annobar ta nuna cewa, ra'ayin bangare guda ba shi da wani alfanu, ya bayyana hakan ne a babban taron muhawara na kwamitin sulhun MDD game da sha'anin tafiyar da shugabancin duniya bayan annobar COVID-19. Faki ya ce, annobar ta kara share hanyar tabbatar da tsarin gamayyar bangarori daban daban, da kuma bayyana rashin alfanun kafa shinge da wasu mambobin kasashe ke kokarin yiwa 'yan Adam wadanda tamkar iyali guda ne. Ya ce, Afrika ta bukaci kowane bangare ya nuna jajurcewa kuma a yi aiki tare da juna wajen tabbatar da farfadowar tsarin gamayyar bangarori daban daban, wanda shi ne manufar kungiyar AU. Tabbas, za mu iya cewa baki ya zo daya tsakanin Sin da Afrika kan wannan muhimmin ra'ayi na neman tabbatar da hadin gwiwar bangarori daban daban. Hakika, wannan manufa za ta taimaka wajen tabbatar da hadin kan duniya, da zaman lafiya, da tsaro, da kuma samun zaman lafiya da lumana gami da bunkasuwar tattalin arziki a duniya. (Ahmad Fagam)