logo

HAUSA

Daryl Morey ya yi murabus daga aikin manajan kungiyar Houston Rockets

2020-10-16 17:39:05 CRI

Daryl Morey ya yi murabus daga aikin manajan kungiyar Houston Rockets

Shekara daya bayan da ya ba da ra'ayin da bai dacewa ba game da yankin Hong Kong na kasar Sin, manajan kungiyar wasan kwallon kwando ta Houston Rockets ta kasar Amurka Daryl Morey ya sanar da yin murabus daga aiki a yau. An gabatar da cikakkiyar sanarwar yin murabus din Morey a shafin internet na kungiyar Houston Rockets, inda ya bayyana cewa, zai janye daga aikinsa na manajan kungiyar a ranar 1 ga watan Nuwanba a hukumance. Ya ce bayan da ya dawo daga Orlando, ya waiwayi shekaru 14 da ya yi yana aiki a kungiyar Houston Rockets, kuma ya tattauna tare da iyalansa da abokansa, kana ya tsaida kudurin cewa, zai bar kungiyar tun daga ranar 1 ga watan Nuwanba. An ce, bayan da kungiyar Los Angeles Lakers ta doke kungiyar Houston Rockets, ta kuma shiga wasan karshe na gasar wasan kwallon kwando ta yankin yammacin kasar Amurka, Morey ya gaya wa shugaban kungiyar Houston Rockets Tilman Fertitta ra'ayinsa, na yin murabus daga aikin manajan kungiyar. Tun daga shekarar 2007, Daryl Morey yake matsayin manajan kungiyar Houston Rockets ta kasar Amurka, har zuwa yanzu, inda ya shafe tsawon kaka 13, daidai da shekaru 14 ke nan yana aiki da kungiyar.

Daryl Morey ya yi murabus daga aikin manajan kungiyar Houston Rockets

Idan ba a manta ba, a watan Oktoba na shekarar 2019, yayin da Morey yake ziyara tare da kungiyar a birnin Tokyo na kasar Japan, ya wallafa wani hoto a shafin sa na twitter, inda ya yi bayanin da bai dace ba dangane da batun Hong Kong na kasar Sin. Lamarin da ya sa masu sha'awar kungiyar Houston Rockets na kasar Sin sun fusata, sun kuma nuna kin amincewa da shi sosai. Daga baya kuma, kafar gabatar da shirye-shiryen wasannin motsa jiki karkashin babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), ta sanar da dakatar da gabatar da gasannin wasan da kungiyar Houston Rockets ke bugawa, kafin a kai ga dakatar da dukkan gasannin wasan kwallon kwando na NBA a dukkan kasar Sin. Kana wasu kamfanonin kasar Sin masu yin hadin gwiwa tare da kungiyar Houston Rockets, su ma sun sanar da yanke hadin gwiwarsu a lokacin.

Hong Kong yanki ne na kasar Sin, kuma harkar Hong Kong harkar cikin gida ce ta kasar, kuma al'ummar kasar Sin ba za su hakuri da duk wanda ya tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong da kuma harkokin cikin gida na kasarsu ba. Mr Morey, Ala Raka Taki Gona!(Zainab Zhang)