logo

HAUSA

HADIN GWIWA DA AIKI TARE NE KASHIN BAYAN YAKAR CUTAR COVID-19

2020-10-15 15:54:31 CRI

HADIN GWIWA DA AIKI TARE NE KASHIN BAYAN YAKAR CUTAR COVID-19

A yayin da cutar COVID-19 ke ci gaba da bazuwa a sassan duniya daban daban, take kuma ci gaba da barazana ga tsarin kiwon lafiyar bil Adama, da tattalin arziki da zamantakewar al'umma, masharhanta da dama na ci gaba da bayyana bukatar yin hadin gwiwa tsakanin sassan duniya, wajen daukar matakai na bai daya, domin shawo kan wannan annoba cikin nasara. Ta dai bayyana a fili cewa, ba wata kasa guda daya tilo a duniya, da za ta iya shawo kan wannan annoba ita kadai, sai dai fa idan kasashen duniya sun zamo tsintsiya madaurinki daya wajen daukar matakai tare. Hakan ne ma ya sa a yanzu haka, kasashen duniya da dama suka shiga wani babban shiri mai lakabin COVAX, na samar da rigakafin cutar cikin hadin gwiwa, musamman don kasashe masu rauni da matalauta, karkashin hukumar lafiya ta duniya WHO. To sai dai kuwa duk da haka, wannan shiri yana fuskantar kalubale na rashin goyon baya daga wasu manyan kasashen duniya. Alal misali, a baya bayan nan, mujallar "The New England Journal of Medicine" ta Amurka, ta wallafa wani sharhi mai taken "Rasa rayuka karkashin rashin jagoranci," wanda ya yi suka game da yadda mahukuntan kasar Amurka suka gaza ta ko wane fanni, game da daukar matakan shawo kan cutar ta COVID-19. Sharhin ya soki 'yan siyasar kasar, game da rikon sakainar kasha da suka rika yiwa batun cutar, da siyasantar da shi, wanda hakan ya kai ga cutar ta yiwa kasar kamun kazar kuku.

HADIN GWIWA DA AIKI TARE NE KASHIN BAYAN YAKAR CUTAR COVID-19

Sharhin ya kara da cewa, duk da yake kawo yanzu, masu bincike da masanan kiwon lafiya, ba su kammala tantance dabarun rigakafi ko magancewa cutar baki daya ba, amma a hannu guda, abun da kowa ya sani shi ne matakan kandagarki, da na yin gwaji a kai a kai, da sanya marufin baki da hanci, da ba da tazara, suna taka muhimmiyar rawa wajen dakile bazuwarta.

Bugu da kari, musayar bayanai na gaskiya, da samar da tallafi ga sassan da ke cikin matsananciyar bukata, domin rage kaifin cutar a sassan duniya daban daban, da hadin gwiwa wajen tunkarar kalubalen magance cutar a mataki na kasa da kasa tsakanin kwararru da sauran shugabanni masu tsara manufofi, na cikin muhimman dabaru da masana suka sha nanatawa, wadanda ka iya baiwa duniya kariya daga mummunan tasirin ta.

Amma abun tambaya a nan shi ne, shin ko kasashen dake daukar matakai na kashin kai za su farga kafin lokaci ya kure? (Saminu Alhassan)