logo

HAUSA

Shenzhen na kara kirkiro abubuwan al'ajabi ta hanyar kirkire-kirkire

2020-10-15 20:35:35 CRI

Shenzhen na kara kirkiro abubuwan al'ajabi ta hanyar kirkire-kirkire

Yayin babban taron murnar cika shekaru 40 da kafa yankin tattalin arziki na musamman na Shenzhen a jiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, dole ne a kara mai da hankali kan kirkire-kirkire yayin da ake gudanar da juyin juya halin kimiyya da fasaha da sauye-sauyen sana'o'i a fadin duniya, hakika ci gaban Shenzhen daga karamin gari zuwa babban birnin dake nuna fifiko wajen ci gaban kimiyya da fasaha ya samo asali ne daga kirkire-kirkire.

Kafin shekaru 40, a farkon kafa birnin Shenzhen, kusan babu albarkatun kimiyya da fasaha a birnin, injiniyoyi guda biyu ne kawai a fadin birnin, amma yanzu birnin yana sahun gaba a fannin kirkire-kirkire, adadin kamfanonin kimiyya da fasaha na zamani da aka kafa a birnin ya zarta dubu 30, manyan kamfanoni dake birnin sun hada Huawei da CGN da Tencent da BYD, kana an fitar da matakan kwaskwarima sama da 1000 a birnin a cikin shekaru 40 da suka gabata, duk wadannan sun shaida cewa, ana kara zurfafa kwaskwarima daga duk fannoni a birnin na Shenzhen. Abun faranta rai shi ne, a cikin wadannan shekaru 40, mazauna Shenzhen suna sauya "kirar kasar Sin" zuwa "kirkirar kasar Sin", yanzu ana amfani da fasahar 5G da motocin dake aiki da sabbin makamashi da sauransu, kuma adadin neman samun 'yancin mallakar fasaha na mazauna Shenzhen dubu 10 ya kai 106.3, adadin da ya ninka sau 8 bisa matsakaicin matsayin kasar Sin, ko shakka babu Shenzhen yana sahun gaba a fannin kirkire-kirkire a fadin kasar Sin. An cimma wannan nasarar ce, saboda yadda kasar Sin ta aiwatar da namufar bude kofa ga ketare da kuma yin kwaskwarima a gida, haka kuma Shenzhen ya samu ci gaba cikin sauri ne domin ya yi kokarin shiga tsarin sana'o'in kasa da kasa, ana iya cewa, kullum Shenzhen yana bisa hanya yayin da yake kokarin raya tattalin arzikinsa, wato ya bude kofarsa ga ketare tare kuma da yin kirkire-kirkire, har ya kai sahun gaba a fannin kimiyya da fasaha.

Yanzu haka birnin Shenzhen yana ci gaba da kara bude kofa ga waje da kuma kara zurfafa yin gyare-gyare a gida, kuma yana kokarin shiga tsarin kirkire-kirkiren duniya, domin kirkiro karin abubuwan al'ajabin da za su taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya.(Jamila)