logo

HAUSA

'Yan siyasar Amurka dake nuna bangaranci sun aikata manyan laifukan keta hakkin dan Adam

2020-10-08 21:15:59 CRI

'Yan siyasar Amurka dake nuna bangaranci sun aikata manyan laifukan keta hakkin dan Adam

Kwanan nan, ana ta ka-ce-na-ce kan batutuwan da suka shafi hakkokin dan Adam a wajen taron kwamiti na uku na babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 75, inda Amurka da sauran wasu kasashe 'yan kalilan, suka shafawa kasar Sin bakin fenti, abun da ya jawo babbar adawa daga kasar ta Sin. Haka kuma, akwai kasashe kusan 70 wadanda suka goyi bayan kasar Sin, abun da ya rushe yunkurin Amurka na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da batun hakkin dan Adam. Wannan ita ce nasarar da ra'ayin kasancewar bangarori daban-daban ya sake samu kan ra'ayin nuna bangaranci a wajen MDD. Akwai wasu 'yan siyasar kasar Amurka, wadanda suka dauki matakan soja ko sanya takunkumi na kashin kai kan wasu kasashe, abun da ya kawo babbar illa ga ci gaban tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma a kasashen, har ma ana ta keta hakkokin al'ummunsu daga dukkan fannoni.

'Yan siyasar Amurka dake nuna bangaranci sun aikata manyan laifukan keta hakkin dan Adam

A halin yanzu, wasu kasashe marasa ci gaba, musamman kasashen da suka jima suna fuskantar takunkumi daga kasashen yammacin duniya, suna fuskantar babban kalubale na hana yaduwar COVID-19, wadanda ke bukatar tallafin kasa da kasa. Amma 'yan siyasar Amurka ba su tausaya musu ko kadan ba, har ma suna yunkurin saka batun siyasa a cikin annobar, da kara sanya musu takunkumi, domin cimma burinsu na kara kawo tashe-tashen hankali da rura wutar kyama, har ma da kifar da gwamnati.

A wajen taron, a madadin wasu kasashe 26, kasar Sin ta sake jaddada cewa, hadin-gwiwar kasa da kasa muhimmin makami ne wajen samun galaba kan annobar COVID-19, don haka kamata ya yi a kawar da matakan tilas na kashin kai, da tabbatar da cewa kasa da kasa sun tinkari annobar yadda ya kamata. Irin wannan matsayi da gwamnatin kasar Sin take da shi, ya bayyana fatan al'ummun kasa da kasa. (Murtala Zhang)