logo

HAUSA

Alkawarin kasar Sin ta ganin kasashe masu tasowa sun fara cin gajiyar riga kacin COVID-19 na nan daram

2020-10-07 14:44:35 CRI

Alkawarin kasar Sin ta ganin kasashe masu tasowa sun fara cin gajiyar riga kacin COVID-19 na nan daram

A yayin da har yanzu duniya ke fama da annobar COVID-19, a hannu guda kuma masana lafiya na can na gudanar da bincike, don ganin an samar da alluran riga kafin wannan annoba da ke ci gaba da addabar duniya. Yanzu haka bayanai na nuna cewa, kasashen duniya, ciki har da kasar Sin sun shiga matakai daban-daban na samar da wannan riga kafi. Sai dai tun ba a je ko'ina ba, wasu kasashen yamma, sun nuna bukatarsu ta fara jin gajiyar riga kafin, maimakon yin raba dai-dai ko wadatar da dukkan kasashe ko wadanda ke da rauni a fannin kayayyakin kiwon kafiya. Abin da malam Bahaushe ke cewa, kashin Dankali, Babba a kan karami. Amma sabanin son kai da ma yadda kasashen yamma ke son yin amfan da riga kafin a matsayin wani makami na siyasa, ita kuwa kasar Sin, tana kokarin ganin ta samar da alluran riga kafin COVID-19, a kokarin da duniya ke yi na ganin bayan annobar. Kasar Sin ta kuma sha bayyana cewa, bayan ta yi nasarar kammala gudanar da binciken samar da rigakafin, da ma fara amfani da ita, ta yi alkawarin fara samar da riga kafin ne ga kasashe masu tasowa ta hanyoyi daban-daban, ciki har da ba da gudummawa da kuma taimakawa kyauta. Matakin da masana ke cewa, ita ce ma'anar yin hadin gwiwa da cin moriya tare. A yayin da kasar Sin ke kokarin cimma wannan muhimman buri, a baya-bayan nan kuma, wasu kafofin watsa labarai sun ba da rahoton cewa, wai farashin alluran rigakafin a kasar Sin ya fi na Turai da Amurka tsada sosai. Koda yake babu kamshin gaskiya kan wannan magana.

Sanin kowa ne cewa, hukumar lafiyar duniya ta WHO ta sha yin kira ga kasashen duniya da su kaucewa yin fito na fito kan batutuwan dake shafar nazari da samar da allurar rigakafi, ya kamata su karfafa hadin gwiwa, domin fuskantar kalubaloli tare, ta yadda za a gaggauta ayyukan samar da allurar rigakafi kamar yadda ake fata, domin a gudu tare a tsira tare. Idan kunne ya ji, to Gangan jiki ya tsira.(Ibrahim Yaya)