logo

HAUSA

Sabon tsarin ci gaban kasar Sin na inganta farfadowar tattalin arzikin duniya

2020-10-03 17:14:13 CRI

Sabon tsarin ci gaban kasar Sin na inganta farfadowar tattalin arzikin duniya

 

A lokacin hutu na bikin kasa da na bikin tsakiyar yanayin kaka bisa kalandar gargajiya ta manoman kasar Sin na bana, Sinawa da suka samu ci gaba wajen yakar cutar COVID-19 suna kara nuna sha'awarsu kan sayayya. Karuwar masu sayayya na amfani wajen kafa wani sabon tsarin ci gaba dake mayar da hankali kan raya tattalin arziki a cikin gida, tare kuma da hade kasuwar cikin gida da ta ketare. Irin tsarin dake bada muhimmanci kan raya tattalin arziki a cikin gida, na nufin mai da habaka bukatun cikin gida matsayin wani babban tushe, kuma bisa wannan tushe ne za a inganta ci gaban tattalin arziki mai inganci.  

Sabon tsarin ci gaban kasar Sin na inganta farfadowar tattalin arzikin duniya

 

Abin lura a nan shi ne, sabon tsarin ci gaba ba ya nufin raya tattalin arziki a cikin gida kadai, a maimakon haka, yana nufin tsarin dake hade kasuwar kasa da ta ketare, ta hakan, za a karfafa mu'amala tsakanin kasar Sin da tattalin arzikin duniya baki daya. Da farko, ko shakka babu, kara habaka bukatun cikin gida, zai kawo dama ga duniya, ciki har da kawo karuwar bukatu, kara samar da kasuwa da zuba jari ga sauran kasashe, da dai sauransu. Na biyu, gudanarwar tsarin masana'antun kasar Sin yadda ya kamata zai amfanawa gudanar tsarin sana'o'in duniya yadda ya kamata.

"Kasar Sin ba za ta rufe kofarta ba, sai ma dai ta kara bude kofar."Ko da yake ana fuskantar yaduwar COVID-19, da koma bayan tattalin arzikin duniya, kasar Sin za ta ci gaba da kaddamar da sabbin matakan kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare.

A matsayinta na kasar dake gaba a duniya a fannonin kandagarkin cutar COVID-19 da farfado da tattalin arziki, kasar Sin za ta kara saurin kafa sabon tsarin ci gaba, don kara habaka sabbin fannonin ci gaban tattalin arziki, har ma da inganta farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya. (Mai fassara : Bilkisu)