logo

HAUSA

Shirin kasar Sin muhimmin karfi ne na tabbatar da daidaiton jinsi a duniya

2020-10-02 18:32:41 CRI

Shirin kasar Sin muhimmin karfi ne na tabbatar da daidaiton jinsi a duniya

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a jiya 1 ga wata ta kafar bidiyo, a wajen babban taron MDD na tunawa da cika shekaru 25 da shirya babban taron mata na kasa da kasa a Beijing, inda ya gabatar da wasu muhimman shawarwari hudu dangane da raya harkokin mata a duniya, tare da sanar da wasu matakan kasarsa na kara tallafawa harkokin da suka shafi mata a duniya nan da shekaru biyar masu zuwa. A matsayin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin ta yi bakin kokarinta, sannan ta samu nasarori da dama a fannin shimfida daidaiton jinsi. Kawo yanzu, Sin ta kafa wani ingantaccen tsarin tabbatar da hakkokin mata, ciki har da zartas da dokoki sama da 100.

Shirin kasar Sin muhimmin karfi ne na tabbatar da daidaiton jinsi a duniya

Domin kara goyon-bayan ci gaban harkokin matan duniya, shugaba Xi ya sanar da wasu matakan da kasarsa za ta dauka nan da shekaru biyar dake tafe, ciki har da kara samar da kyautar kudi da yawansa ya kai dala miliyan 10 ga hukumar mata ta MDD , da ci gaba da bayar da lambar yabo ta Sin da UNESCO kan aikin bada ilimi ga yara mata da 'yan mata. Kana shugaba Xi yana kira da a sake gudanar da taron kolin kasa da kasa kan harkokin mata nan da shekaru biyar masu zuwa, al'amarin da ya shaida cewa kasar Sin tana da hangen nesa da maida hankali sosai kan bunkasuwar harkokin mata a duniya.

A halin yanzu cutar COVID-19 na ci gaba da addabar duniya, akwai bukatar raya duniya da babu bambancin ra'ayi ko wariyar da ake nunawa mata. In dai an cimma wannan buri, za'a kara samun wayewar kai, har ma zamantakewar al'umma za ta ci gaba da kyautata.(Murtala Zhang)