logo

HAUSA

Me yasa Amurkawa suka dena gaskata shugabanninsu da hukumomin yaki da annobar COVID-19 na kasar

2020-09-28 16:16:58 CRI

Me yasa Amurkawa suka dena gaskata shugabanninsu da hukumomin yaki da annobar COVID-19 na kasar

Masu hikimar magana na cewa, "idan tsoho banji kunyar hawa jaki ba, to shi ma jakin ba zai ji kunyar kayar da tsoho ba". A bayyane take, al'amarin tsarin demokaradiyyar Amurka lamari ne mai cike da sarkakiya gami da rashin tabbas. Musamman idan aka yi la'akari da salon shugabancin mahukunta gwamnatin kasar. Koda yake, batun salon kamun ludanyin shugaban kasar mai ci a halin yanzu ya jima yana tada kura da cece-kuce a fagen siyasar duniya bisa la'akarin da halayyarsa na yin tufka da warwara.

Sai dai, babban abin takaici ne yadda al'ummar kasar Amurka suka dawo daga rakiyar shugaban kasar Donald Trump, musamman game da batun yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19. Koda a kwanan baya ma, wani rahoton binciken da aka gudanar na baya bayan nan kan wasu daidaikun mutane sama da 21,000 tsakanin 7 zuwa 26 ga watan Ogasta ya nuna cewa, jama'ar kasar Amurka sun yanke kauna da kuma kin yarda da gwamnatin kasar da hukumomi 15 dake tafiyar da ayyukan yaki da annobar COVID-19 a kasar ta Amurka, a cewar binciken an fara samun rashin yardar ne tun daga watan Afrilu har zuwa Ogasta, kamar yadda labaran da aka watsa a shafin intanet na jami'ar Northwestern University NU, ya bayyana.

Wannan rahoton bincike ya nuna cewa, yadda mutanen kasar suka dena yarda da maganganun shugaban kasar, da kuma yadda shugaban kasar Donald Trump ke tafiyar da yaki da annobar COVID-19 ya ragu daga kashi 50% a karshen watan Afrilu zuwa kashi 43% a watan Ogasta, koda yake, adadin ya dan karu da maki biyu daga watan Yuli. Rashin yardar ya faru ne game da cece-kucen da Amurkawa ke yi game da ko Amurkawan za su karbi rigakafin annobar COVID-19 idan an samar da shi. Mutane 6 cikin 10 ko kuma kashi 59 bisa 100 na binciken da aka gudanar sun bayyana cewa, za su amshi rigakafin na COVID-19, sai dai an sake samun raguwar maki 7 daga kashi 66% a karshen watan Yuli.

Banbance-banbance game da wanda ya dace a yiwa rigakafin yana da alaka ta kut-da-kut da yadda mutane suka amince da shugabanni da kuma cibiyoyin yaki da annobar a kasar. Ko ma dai wane irin martani Amurkewa suka mayar kan gwamnatin shugaban kasar mai ci, batu ne da masu hikimar magana ke cewa, "kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa". A wani kaulin kuma, an ce "dama na san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya". (Ahmad Fagam)