logo

HAUSA

Dauwamammen Zaman Lafiya A Xinjiang Ya Rusa Yunkurin Wasu 'Yan Siyasar Amurka Na Amfani Da Batun Jihar Don Hana Ci Gaban Kasar Sin

2020-09-27 21:24:22 CRI

Dauwamammen Zaman Lafiya A Xinjiang Ya Rusa Yunkurin Wasu 'Yan Siyasar Amurka Na Amfani Da Batun Jihar Don Hana Ci Gaban Kasar Sin

A wajen taron sanin makamar aiki kan jihar Xinjiang da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya karo na uku, shugaban kasar Xi Jinping ya takaita nasarorin da aka samu wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a jihar, tun bayan da aka shirya irin wannan taro a karo na biyu a shekara ta 2014, inda ya kuma tsara wasu muhimman manufofi kan tabbatar da zaman karko da kwanciyar hankali mai dorewa a wurin. Daga shekara ta 2014 zuwa ta 2019, matsakaicin karuwar yawan GDPn jihar Xinjiang ya kai kaso 7.2 bisa dari a kowace shekara, kuma matsakaicin kudin shiga da kowane mutum zai iya amfani da shi ya karu da kaso 9.1 bisa dari. Haka kuma an yi hasashen cewa, za'a fitar da dukkan mutanen jihar Xinjiang daga kangin talauci a karshen shekarar da muke ciki. Sa'an nan kuma a cikin shekarun shida, gwamnatin kasar Sin ta ware kasafin kudi da yawansa ya zarce Yuan tiriliyan 2 domin tallafawa jihar ta Xinjiang. Dukkan wadannan alkaluman sun shaida cewa, an samu dimbin nasarori wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a Xinjiang, wadanda ba'a taba ganin irinsu ba a tarihi, kuma al'ummar jihar suna kara jin dadin zaman rayuwarsu.

Dauwamammen Zaman Lafiya A Xinjiang Ya Rusa Yunkurin Wasu 'Yan Siyasar Amurka Na Amfani Da Batun Jihar Don Hana Ci Gaban Kasar Sin

A wajen taron kuma, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ya dace a hada kokarin bude kofar Xinjiang da kokarin bude kofar kasar Sin tare, abun da ya kafa alkibla ga ci gaban jihar a nan gaba.

Amma duk da haka, akwai wasu 'yan siyasar kasar Amurka, wadanda suke yunkurin bata sunan kasar Sin bisa fakewa da hakkin dan Adam ko batun kabila ko kuma addini. A wajen muhawarar da aka yi a gun taro na 45 na kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD wanda aka yi kwanan baya, wakilai daga kasashe da dama sun gabatar da jawabai, inda suka bukaci wasu kasashe da su dakatar da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin.

Kome rintsi daukacin al'ummar kasar Sin da yawansu ya kai biliyan 1.4 ba za su amince da yunkurin wasu 'yan siyasar Amurka na kawo baraka ga kasar Sin ba. Wato babu wanda zai iya hana kokarin al'ummar jihar Xinjiang na neman ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a jihar. (Murtala Zhang)