logo

HAUSA

Amurka mai kalubalantar zaman lafiyar duniya

2020-09-26 20:22:58 CRI

Amurka mai kalubalantar zaman lafiyar duniya

Cikin taron muhawarar MDD karo na 75, shugaban kasar Amurka ya gabatar da jawabin dake cike da bambancin ra'ayi da karya. Mai iyuwa, karfin sojan kasar ya bai wa shugaban imamin yada manufarta ta "Amurka da farko", amma, yadda yake nuna ra'ayin son kai, ya bata ran gamayyar kasa da kasa kwarai da gaske.

Idan ba a manta ba, a watan Mayun shekarar 2018, kasar Amurka ta sanar da janye jiki daga yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, amma, kwanan baya, ministan harkokin wajen kasar Mike Pompeo ya gabatar da bukata ga MDD, domin farfado da takunkumin da aka kakabawa kasar Iran cikin sauri, lamarin da ya fuskanci adawa daga galibin mambobin kwamitin sulhu na MDD. Sai dai, kasar Amurka ta fara kakabawa kasar Iran takunkumi da kanta, lamarin da ya bata ran kasa da kasa, yayin da ya nuna halinta na kawo barazana ga zaman lafiya da zaman karkon kasa da kasa. Kana, jawabin da shugaban kasar Amurka ya yi cikin taron muhawarar MDD, ya nuna kaunar wannan kasa kan manufar "Amurka da farko", wasu 'yan siyasan kasar Amurka sun kuma yi amfani da wannan manufa wajen kawo barazana ga kasa da kasa, lamarin da ya bata tsarin kasa da kasa, da ma zaman lafiyar duniya.

Shi ya sa, cikin wannan taron muhawarar MDD, aka yi kira ga kasa da kasa da su yi alkawarin goyon bayan tsarin hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban, domin mai da martani kan matakin kashin kai da kasar Amurka ta dauka. Ya kamata a dukufa wajen kawo karshen wasan siyasa da kasar Amurka take yi. (Maryam Yang)