logo

HAUSA

Komai Rintsi Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan MDD

2020-09-24 15:45:35 CRI

Komai Rintsi Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan MDD

Da yammacin jiya Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da babban magatakardar MDD Antonio Guterres ta kafar bidiyo, inda ya jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka, wajen goyon bayan ayyukan majalisar, yana kuma fatan sassan kasa da kasa za su kara karfafa cudanyar dake tsakaninsu, ta yadda za a gina kyakkyawar makoma ga dukkanin bil Adama.

Wadannan kamalai muhimmai da shugaban na Sin ya ambata, ga dukkanin mai bibiyar manufofin kasar Sin, zai lura cewa, suna dada jaddada matsayar kasar ta Sin ne, kasancewar ta kasa mai matukar goyon bayan ra'ayin cudanyar bangarori daban daban, wadda ke fatan kasashen duniya za su yi watsi da ra'ayin ware kai, ko bin ra'ayin kashin kai, da kariyar cinikayya, da nuna kyama ko nunawa saura fifiko. Ko da a kalaman sa, yayin da yake jawabi ga zaman mahawarar MDD, a gabar da majalissar ke cika shekaru 75 da kafuwa, shugaba Xi ya sako batun hadin gwiwar kasa da kasa, musamman ma a gabar da duniya ke fuskantar manyan kalubale, ciki hadda na yaki da cutar numfashi ta COVID-19. Muna iya kara fahimtar kasar Sin, da muradun shugabannin ta, don gane da goyon baya da martaba ka'idojin MDD. Masharhanta da dama na ganin cewa, tun bayan kafuwar majalisar, ta samu babban sakamako a fannin shimfida zaman lafiya a fadin duniya, yayin da kuma a gefe guda, kasar ta Sin ke ci gaba da tsayawa tsayin daka, wajen goyawa MDDr baya. Masana da dama na ganin cewa, da ace dukkanin kasashen duniya, musamman masu karfin fada a ji, za su rungumi wadannan manuofi na kasar Sin na "A gudu tare a tsira tare", da hakan ya haifar da manyan nasarori ga ci gaban rayuwar bil Adama daga dukkanin fannoni.

Ko shakka ba bu, duniya na fuskantar manyan matsaloli da ke matukar bukatar hadin kan kasa da kasa wajen warware su, kuma ba wata dabara da ta wuce hadin kai, da goyawa juna baya, wajen shawo kan duk wani lamari dake zamewa duniya "Kadangaren bakin tulu", tun da dai bil Adama, ba shi da wata duniya ta daban in ban da wadda muke rayuwa a cikin ta, don haka fatan shi ne sauran shugabannin kasashe, da yankunan duniya, za su amince cewa "Yiwa wani yiwa kai ne", su goyi bayan ayyukan MDD yadda ya kamata, don kaiwa ga tudun mun tsira tare. (Saminu Hassan)