logo

HAUSA

Karfin kasar Sin na da babban tasiri wajen tallafawa cudanyar sassa daban daban

2020-09-23 20:44:05 CRI

"Shekaru 75 da suka gabata, kasar Sin ta bayar da babbar gudummawa a fannin cimma nasarar yaki da 'yan mulkin danniya, ta kuma tallafa wajen kafa MDD. A yau, a kokarinta na kiyaye wannan moriya, Sin na ci gaba da shiga hadin gwiwar kasa da kasa a fannin kandagarki da shawo kan annobar COVID-19, tana kuma ba da gudummawa wajen samar da tsaron lafiya a mataki na kasa da kasa."

Karfin kasar Sin na da babban tasiri wajen tallafawa cudanyar sassa daban daban

Yayin babbar muhawara da aka bude a zauren babban taron MDD jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi, wanda a cikinsa ya bayyana kudurin kasarsa, na aiki tare da kasashen duniya, don tunkarar kalubalolin da duniya ke fuskanta, ciki hadda annobar COVID-19.

A halin da ake ciki, annobar COVID-19 ita ce babban kalubale da duniya ba ta taba ganin irin ta ba cikin dukkanin wannan karni, ta kuma jefa makomar bil Adama cikin wani mawuyacin hali. Wani abun damuwar ma shi ne, yadda wasu manyan kasashen duniya ke rungumar ra'ayin ware kai, da kaucewa shiga hadin gwiwar kasa da kasa a fannin kandagarki da shawo kan cutar COVID-19, wanda hakan ka iya yin mummunan tasiri ga yanayin da ake ciki bayan yake-yake, duba da cewa, burin dakile hakan ne ya haifar da MDD tun da fari. A daidai wannan gaba ta tarihi, taken dandalin babban taron MDD ya karkata ne ga batun cudanyar dukkanin sassa, wanda shi ne buri mafi muhimmanci. A matsayinta na kasa dake kan gaba wajen aiwatar da matakan kandagarki da shawo kan COVID-19, tare da bunkasa farfadowar tattalin arziki, Sin ya kasance a sahun farko wajen baiwa manufar cudanyar sassa daban daban goyon baya. A cikin jawabin da ya gabatar, Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda 4, wadanda ke jaddada bukatar amincewa da manufar sanya rayukan mutane gaba da komai, da karfafa hadin kai, da taimakawa juna yayin da ake tunkarar matsala iri daya.

Karfin kasar Sin na da babban tasiri wajen tallafawa cudanyar sassa daban daban

Kaza lika ya gabatar da shawarar samar da wani cikakken tsari mai kunshe da dabarun aiwatar da kandagarki da shawo kan annobar COVID-19 a hukumance. Sai kuma batun taimakawa kasashe masu tasowa a wannan fanni, musamman ma kasashen Afirka. Dukkanin wadannan shawarwari dai sun dace da wasu shawarwarin da a baya shugaban na Sin ya gabatar.

Shugaban na Sin ya ce "yanzu haka an mika mana damar sarrafa zamanin mu. Don haka ya dace mu yi zabi mafi dacewa da al'ummun mu, daidai da irin tarihin da muke fatan bari." Wadannan kalmomi na shugaba Xi sun haifar da zuzzurfan tunani.

Sin wadda har kullum ke nacewa manufar cudanyar dukkanin sassa, za ta ci gaba da zama mai tallafawa shirin wanzar da zaman lafiyar duniya, mai ba da gudummawa ga ci gaban duniya, kana mai ba da kariya ga tsarin cudanyar duniya. Bugu da kari za ta raba dabarunta, da kwarewa, da karfinta a fannin karfafa yakin da duniya ke yi da annoba, da ma sauran kalubale na yau da kullum. (Saminu Hassan)