logo

HAUSA

Zama tsintsiya madaurinki daya, shi zai kai duniya ga shawo kan kalubalen da take fuskanta

2020-09-22 17:25:38 CRI

Zama tsintsiya madaurinki daya, shi zai kai duniya ga shawo kan kalubalen da take fuskanta

A jiya Litinin ne aka kaddamar da taron manyan jami'ai na Majalisar Dinkin Duniya domin tunawa da cikar majalisar shekaru 75 da kafuwa. Taron wanda aka gudanar ta kafar intanet, shi ne irinsa na farko a tarihi, saboda annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Yayin taron, Shugaban kasar Sin Xi Jinping na daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi, inda ya tabo wasu muhimman batutuwa da suka shafi zamantakewar kasa da kasa. Da farko, shugaba Xi Jinping ya yi kira ga MDD ta tashi tsaye wajen tabbatar da adalci. Ya ce mutunta juna tsakanin dukkan kasashen duniya ba tare da la'akari da girmansu ba, shi ne ci gaba a wannan zamanin, kuma shi ne muhimmin ka'idar majalisar. Lallai a wannan zamanin da ake ciki na fuskantar rashin tabbas da kokarin danniya da babakere, akwai bukatar tunatar da manyan kasashe da suke ganin sun samu ci gaba ko sun zama masu fada a ji, su yi kokarin tsare adalci da mutunta kasa da kasa. Karfin arzikin kasa ko ci gabanta, ba zai taba zama ka'idar danniya ko ci da gumin kananan kasashe ba. Bai kamata a rika nuna wariya kawai saboda wasu ba su kai wasu girma ba. Kamar yadda shugaban ya ce, yayin da ake fuskantar sabbin sauye-sauye da kalubale, dole ne a hada hannu don shawo kan matsalolin da ake fuskanta. Shugaba Xi Jinping ya kuma tabo batun girmama dokokin majalisar. Idan dai ana son zaman lafiya da ci gaba, da kuma ba majalisar damar taka rawarta kamar yadda ake muradi, dole ne a tabbatar da girmama dokokin da ta gindaya. Babu yadda za a samu ci gaba da zaman lafiya a tsakanin kasashe idan har wasu na ganin sun fi karfin doka ko biyayya ga ka'idojin da aka gindaya. Bai kamata a ce ana zaune kara zube ba a wannan zamani da ake ciki na wayar kai da ci gaba a duniya. Dole ne manyan kasashe su rika girmamawa da biyayya ga ka'idojin majalisar, ta yadda za su zama abun misali da koyi ga kasashe masu tasowa. Wannan shi zai kara masu kima da daraja, sannan ya ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwar biyayya ga ka'idojin da aka shimfida. Bai kamata wata ko wasu kasashe su rika yin gaban kansu suna keta dokoki, suna ganin kamar sun fi karfin doka ba, kawai saboda sun samu arziki. Wadannan ka'idoji, su suka kafa majalisar, kana sai da dukkan kasashe suka amince da su, don haka, martaba su ya zama wajibi. Har ila yau, shugaban na kasar Sin ya ja hankalin mambobin majalisar game da bukatar hadin kai. A cewarsa, dole ne hawa teburin sulhu ya maye gurbin rikici, sannan moriyar juna ta maye gurbin ci da gumin wani bangare. Hakika dai, idan ana son samun ci gaba da zaman lafiya da mutunta juna, dole ne kasashen duniya su hada kai wuri guda sannan su girmama moriyar juna, ta yadda kowa zai yi kokarin kare muradunsa da na sauran kasashe, ta yadda nasarar wata kasa, za ta zama nasarar baki dayan kasashe, haka zalika asara. Ta wannan hanyar, babu wata kasa da za ta so ganin faduwar 'yar uwarta ko kokarin yi wa wata zagon kasa. Wannan zai kara dankon zumunci da zaman lafiya tsakanin al'ummun duniya. Bugu da kari, Xi Jinpinga ya ce dole ne a yi hobbasa wajen aiwatar da mnufofi a aikace, ba wai su tsaya a fatar baki ba. Lallai ya kamata majalisar ta kara himmantuwa wajen ganin an gudanar da ayyuka a aikace maimakon kawai tsara dabaru a takarda. Zai yi kyau idan aka ga wadannan ayyuka a aikace, lamarin da zai ba al'umma kwarin gwiwar kara ammana da majalisar.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, an shiga wani zamani da muradu da burikan kasashe ke hade da juna, haka zalika makomarsu. Don haka, dukkan kalubalen da ake fuskanta a duniya, na bukatar hadin kai mai karfi daga dukkan kasashe, idan har ana son shawo kansu. Haka kuma ya kamata a kara tunani mai zurfi kan yadda ake son majalsar ta kara taka rawa da sauke nauyin dake wuyanta, bayan kammala yaki da cutar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)