logo

HAUSA

Dabarar Amurka Ta Amfani Da Taiwan Wajen Sarrafa Akalar Sin Ba Za Ta Yi Nasara Ba

2020-09-21 20:39:39 CRI

Kwanan baya, mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka Keith Krach, ya ziyarci yankin Taiwan na kasar Sin, wanda shi ne karo na biyu da gwamnatin Amurka ta aika da manyan jami'anta zuwa Taiwan a bana. Matakin dai ya saba wa ka'idar "kasar Sin daya tak a duniya" da kuma abubuwan da aka tanada cikin hadaddun sanarwoyi guda 3 da kasashen Sin da Amurka suka daddale, kana hakan ya illanta huldar da ke tsakanin kasashen 2, da kuma yanayin kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan. Tabbas kasar Sin za ta mayar da martani, don kiyaye ikon mulkin kasa, da cikakkun yankunan kasar. Wasu 'yan siyasan Amurka, sun hada hannu da 'yan a-ware na Taiwan, don kawar da hankalin Amurkawa daga matsalolin da kasar suke fuskanta a gida, da neman samun ribar siyasa, da hana ci gaban kasar Sin. Hakika dai jama'ar Sin biliyan 1.4, ba za su bari hakan ya yi nasara ba. Ba za a iya hana dinkewar kasar Sin ba. Dabarar 'yan siyasar Amurka ta amfani da Taiwan wajen sarrafa akalar Sin ba za ta yi nasara ba. Al'ummar kasar Sin na da aniya, da karfin zuciya, da kuma kwarewa wajen murkushe yunkurin yin shisshigin da wasu kasashen waje suke yi, da kuma neman haifar da baraka da 'yan a-ware na Taiwan ke fatan samarwa.

Batun Taiwan yana shafar babbar moriyar kasar Sin, wadda take sa kulawa sosai. Haka kuma batu ne mafi muhimanci da jawo hankalin kasar Sin a tsakanin kasashen Sin da Amurka. Ya zama tilas 'yan siyasar Amurka su dakatar da abin da suke yi, su yi taka tsan-tsana, kada su yi kuskuren fahimtar aniyar al'ummar Sin biliyan 1.4, ta kiyaye ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan kasa. Kasar Sin za ta mayar da martani mai karfi kan duk abin da ka illata babbar moriyarta, da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidanta. Tabbas ne wanda ya sa wuta ya kone kansa. (Tasallah Yuan)