logo

HAUSA

Jami'ar Southeast da daliban ketare suna yaki da cutar COVID-19 tare

2020-06-11 14:21:14 cri

Bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, jami'ar Southeast ta birnin Nanjiang na kasar Sin, ta kafa wani tsarin samar da cikakkun bayanan daliban da suka zo jami'ar karatu daga kasashen ketare, domin kara fahimtar yanayin zaman rayuwar dalibai a jami'a, da lafiyarsu cikin lokaci, tare da ba su taimakon da suke bukata. Haka kuma, daliban kasashen ketare dake jami'a sun shiga aikin yin kandagarki, da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 cikin himma da kwazo.

Dalibin jami'ar Carvalho Vladmir Husni Da Costa De, wanda ya zo daga kasar Cape Verde ta nahiyar Afirka, ya dauka wani bidiyo mai taken yadda ake yin kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, domin kara sanin abokan karatunsa game da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma yadda za a yi kandagarkin cutar.  

Jami'ar Southeast da daliban ketare suna yaki da cutar COVID-19 tare

Gaba daya akwai daliban kasashen ketare sama da dubu 1 dake karatu a Jami'ar Southeast ta birnin Nanjing. A lokacin barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, akwai daliban kasashen ketare kimanin dari 2 dake zaune a jami'ar, ciki har da 'yan kasashen Afirka guda 85. Yin Guo wadda ke aiki a ofishin daliban kasashen ketare na jami'ar ta bayyana cewa, jami'ar ta kafa kungiyoyi da dama ta manhajar Wechat, domin samar wa dukkanin daliban ketare labaran dake shafar cutar numfashi ta COVID-19, da kuma sauraron bayanai daga daliban cikin lokaci. A sa'i daya kuma, jami'ar ta kira wani sabon tsarin gabatar da lafiyar jiki, domin tabbatar da lafiyar dukkanin daliban kasashen ketare dake zaune a jami'ar.

"Mun samar da tsarin gabatar da lafiyar jiki da harshen Turanci, ta yadda dukkanin dalibai za su gabatar da yanayin lafiyar jikinsu a ko wace rana, kamar inda suke, zafin jikinsu da wasu harkokin musamman da dai sauransu."

Carvalho Vladmir Husni Da Costa De shi ne dalibin digiri na uku a kwalejin ilmin likitanci na jami'ar, wanda ya riga ya zauna a kasar Sin har shekaru da dama. Bayan karatu, ya kan dauka wasu gajerun bidiyo game da ilmin cutar numfashi ta COVID-19 da kuma gabatar da su ta yanar gizo. Ya ce, wasu daliban kasashen ketare ba su gane matakan da jami'ar ta dauka wajen yin kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ba, domin amsa tambayoyinsu, ya dauka bidiyo na musamman domin bayyana musu dabarun yin kandagarki da dakile yaduwar annobar.

"Wasu abokan karatun mu ba su gane yadda za su yi ba, kuma ba su tabbatar da ko suna yin abun da ya dace ba, shi ya sa su kan tambaye ni, game da yadda za su yi. Shi ya sa na shirya wannan bidiyo, inda bi da bi, na yi bayani game da mene ne kwayar cutar, kuma me ya sa ya dace mu zauna a gida."

Jami'ar Southeast da daliban ketare suna yaki da cutar COVID-19 tare

Bidiyon da ya gabatar ya samu karbuwa sosai, har ma jami'arsa da wasu kafofin watsa labarai sun ruwaito bidiyonsa. Sa'an nan, ya gabatar da karin bidiyo game da yadda cutar numfashi ta COVID-19 yake yaduwa, da yadda ake sanya abun rufe hanci da baki, da kuma yadda ake yin kandagarki, da dakile yaduwar cutar da dai sauran batutuwan dake janyo hankulan al'umma a lokacin yaduwar annobar. Har ma, an fassara bidiyonsa zuwa harshen Turanci da harshen Portugal. Ya ce, ya shirya wadannan bidiyo ne domin ba da taimako ga daliban ketare wajen kara saninsu game da ilmin yin kandagarkin cutar, haka kuma, yana fatan sauran kasashen duniya za su koyi fasahohin kasar Sin na yin kandagarki da dakile yaduwar annobar.

"A ganina, kasar Sin ta kware sosai a fannin killace mutane a gida, sabo da cutar ba za ta iya yaduwa ba, in ba ta yadu daga mutum zuwa wani mutum na daban. Dukkanin matakan da aka dauka a nan kasar Sin, kamar zama a gida, ko kuma killace unguwanni da birane, sun zama matakai da suka dace, wajen dakile yaduwar cutar."

Ya kara da cewa, kwanan baya, jami'ar ta amince daliban ketare su yi taro, domin yin wasu harkokin nishadantarwa, sakamakon nasarorin da aka cimma wajen dakile yaduwar cutar. Ya ji farin ciki sosai dangane da wannan lamari.

Kuma bisa labarin da aka samu, ban da ba da ilmi ta kafar bidiyo, jami'ar ta kuma yin hadin gwiwa da wasu manyan kamfanoni, domin gabatar wa daliban dake dab da gama katarunsu labarai na neman aikin yi, ta yadda za su sami bayanai a kan lokaci. malama Yin Guo ta bayyana cewa,

"Daliban jami'armu suna iya yin rajista ta yanar gizo, domin mu kara sani game da bukatunsu. A sa'i daya kuma, mun kafa tsarin mu'amala da kamfanoni, domin samar da karin bayanai, Sa'an nan, mun gabatar da bayanan ga daliban jami'armu, ta yadda za su samu aikin yi cikin lokaci."

Yanzu, Carvalho Vladmir Husni Da Costa De, yana rubuta rahoton kammala karatunsa. Ya ce, bayan gama karatunsa a kasar Sin, zai koma kasarsa domin yin amfani da ilmin da ya koyo a Sin wajen gina kasarsa, tare kuma ba da gudummawa ga hadin gwiwar harkokin likitanci a tsakanin Sin da Afirka. (Maryam)