logo

HAUSA

Bankin duniya: alkaluman GDP na yankin kudu da hamadar sahara za su sauka da kaso 2.8 a bana

2020-06-10 12:12:55 cri

Bankin duniya ya ce, akwai yuwuwar alkaluman tattalin arzikin yankin kudu da hamadar sahara, su sauka da kaso 2.8 cikin dari a bana, saboda annobar COVID-19.

Bankin ya bayyana haka ne, cikin rahoton hasashen tattalin arzikin bana da ya fitar a jiya Talata. 

Rahoton hasashen tattalin arzikin bana na bankin, ya nuna cewa, ana kuma zaton kudin shigar kowanne mutum a nahiyar Afrika, zai ragu sosai, lamarin da ka iya jefa miliyoyin mutane cikin matsanancin talauci.

Ya kara da cewa, akwai yiwuwar ci gaban tattalin arzikin nahiyar ya karu da kaso 3.1 cikin dari a shekarar 2021, idan annobar ta bace a rabin karshe na bana, kamar yadda sauran annoba na cikin gida ke yi, kana kuma idan aka samu farfadowar manyan harkokin cinikayya.

Rahoton ya kuma yi nazari kan tasirin annobar tare da sakamakon da za su iya haifarwa.

Nazarin ya nuna cewa, a bana, annobar COVID-19 ta dabaibaye nahiyar Afrika, abun da ka iya haifar da koma bayan da ba a taba gani ba a tarihi.

Baya ga mummunan tasirinta kan kiwon lafiya da tsaro, matakan dakile yaduwarta da suka hada da hana tafiye-tafiye da rufe kan iyakoki da kulle, sun kawo tsaiko ga harkokin tattalin arziki na cikin gida.

Bankin ya kara da cewa, raguwar ci gaban manyan harkokin cinikayya da faduwar farashin kayayyaki, sun yi mummunan tasiri a kan harkar fitar da kayayyaki zuwa ketare.

A cewar rahoton, duk da ana sa ran farfadowar harkoki a shekarar 2021, nahiyar ka iya kasancewa cikin gagarumin matsala ta dogon lokaci, duba da rashin ingancin tsarukan kiwon lafiya da manufofin tsuke bakin aljihu, da kuma rashin karfin aiwatar da matakin nisantar juna tsakanin jama'a, kamar yadda ya kamata.

Har ila yau, rahoton ya bayyana cewa, yankin kudu da hamadar sahara na cikin barazanar fadawa tarkon bashi, bisa la'akari da yawan basussukan da ake bin kasashen yankin da kuma bukatar kara ciyo bashin.

Rahoton ya lura cewa, a Nijeriya da Afrika ta kudu, wadanda ke zaman mafiya karfin tattalin arziki a nahiyar, harkokin tattalin arziki sun ragu sosai a rabin farko na bana, yayin da sauran kasashen nahiyar suka shiga mawuyacin hali a wanna lokaci.

Baya ga tsaiko ga harkokin cikin gida, masu fitar da kayayyaki na fuskantar karancin bukatar kayayyakin daga waje da kuma faduwar farashin mai da karafa.

A cewar Bankin, galibin kasashe masu fitar da amfanin gona kamar su Cote d'Ivoire da Habasha da Kenya, suna fama da raguwar bukatar kayayyakin da suke fitarwa da kuma tsaiko a fannin samar da su.

Haka zalika, gagarumar raguwar tafiye-tafiye a duniya saboda annobar, ta yi tasiri mai muni kan kasashen dake samun baki masu yawa saboda yawon bude ido, kamar su Cape Verde da Habasha da Mauritius da Seychelles.

Bugu da kari, rahoton na bankin duniya, ya nuna cewa, galibin kasashen kudu da hamadar sahara, sun sanar da wasu manufofin kudi domin tallafawa harkoki da inganta bangaren kiwon lafiya ta yadda zai shawo kan cutar, sai dai kuma, wannan matakin ya kunshi sake sauya akalar kasafin kudin da aka riga aka yi, saboda manufofin tsuke bakin aljihu. (Fa'iza Mustapha)