logo

HAUSA

Annobar COVID-19 ta matsawa aikin kiyaye dabbobi lamba a Afirka

2020-05-15 12:29:28 cri

Annobar COVID-19 dake ci gaba da bazuwa a duniya ta haifar da illoli ga sana'o'i daban daban, ciki har da aikin kiyaye dabbobi a wasu kasashen Afirka.

Cutar COVID-19 ta yi mummunar illa ga aikin yawon shakatawa a wasu kasashen Afirka. Saboda ana dogaro da aikin yawon sakatawa don samun kudin da ake bukata wajen kula da yankunan kare dabbobi, don haka tsanantar yanayin yaduwar annobar ka iya haddasa karin aikace-aikacen sata da farautar dabbobi a wasu kasashen dake nahiyar Afirka.

John Tanui wani ma'aikaci ne na yankin kare dabbobi na Lewa dake arewacin kasar Kenya. Kimanin kashi 12 % na karkanda mai bakar launi da kasar ke da su, suna zama a cikin wannan yanki na kariya. Mista Tanui ya riga ya kwashe shekaru fiye da 10 yana kula da aikin kare dabbobi. Sai dai, an sallame wasu abokan aikinsa, sakamakon lalacewar tattalin arziki, wani yanayin da annobar COVID-19 ta haddasa. A ganin mista Tanui, wadannan mutane ka iya fara satar dabbobi don samun kudin shiga.

"Idan wadannan mutane suka rasa ayyukansu, to, za su bukaci kudi. Don haka ko zaki ma za su yi kokarin farautarsa. Za su iya farauta da satar karkanda, ko kuma giwa, sa'an nan su sayar da gawawakinsu don neman kudi."

Aikin yawon shakatawa wani ginshiki ne ga tattalin arzikin kasar Kenya, gami da wani muhimmin bangare da ake samun kudi domin tallafawa yankunan kare dabbobi. Kasar Kenya ta kan karbi baki masu yawon bude ido kimanin miliyan 1.5 a duk shekara, kana kaso 70 zuwa 80 daga cikinsu su kan ziyarci wuraren yawon shakatawa gami da yankunan kare dabbobi. A cewar minista mai kula da aikin yawon shakatawa na kasar, sana'ar yawon shakatawa ta kan samar da dalar Amurka biliyan 1.6 ga baitulmalin kasar a kowace shekara, sai dai a bana wannan adadi ka iya sauka zuwa sifiri.

Mista Simba, wani mutum ne da ya kafa asusun kare dabbobi na Mara, wanda ya kwashe shekaru da yawa yana kokarin gudanar da aikin kare dabbobi a kasar Kenya. Shi ma ya gaya ma wakilin CRI cewa, ana fuskatar yiwuwar samun karin aikace-aikacen sata da farautar namun daji.

"Annobar COVID-19 ta gurgunta sana'ar yawon shakatawa a kasashen Afirka. Sa'an nan yankunan kare dabbobi suna dogaro kan yawon shakatawa wajen samun kudi. Don haka, idan babu yawon shakatawa, to, wasu yankunan kariyar dabbobi da yawa za su bace. Za su zama yankunan makiyaya, kana ma'aikata masu kula da aikin kare dabbobi su ma ba za su samu isashen albashi ba. Don haka, za mu iya ganin cewa, annobar tana haifar da mummunan tasiri ga zaman rayuwar jama'ar wadannan wurare, da na ma'aikata masu kula da dabbobi, gami da gurgunta dukkan ayyukan yankunan kare dabbobi baki daya. Mutane da yawa da suka rasa kudin shiga, ba yadda za su yi, kila za su tafi kiwon dabbobi, da kiwon dabba ta wata barauniyar hanya, har ma za su iya fara farauta da satar namun daji."

Hakika kungiyar kare halittu da muhalli ta kasa da kasa ta taba gargadin cewa, cikin wasu watanni 2 bayan barkewar annobar COVID-19 a wasu kasashe, an fara gano karin aikace-aikacen farauta da satar dabbobi a kasashen da suka hada da Kenya, da Cambodia, da dai sauransu.

A matsayin wata dabarar da ake iya dauka don tinkarar wannan matsala, mista Simba ya yi kira ga gwamnatin kasarsa ta ba jama'ar da suke zama a dab da yankunan kare dabbobi damammakin samun kudin shiga, ta wasu hanyoyi masu dacewa. A nasa bangare, John Tanui na fatan ganin bayan cutar COVID-19 cikin sauri, ta yadda masu yawon shakatawa za su koma kasarsa ta Kenya. (Bello Wang)