logo

HAUSA

Labaru game da yadda matasan Wuhan 4 suka yi kokarin dakile annobar COVID-19

2020-05-04 13:53:51 cri

A lokacin da annobar cutar COVID-19 ta bulla a birnin Wuhan ba zato, matasan kasar Sin da suka kunshi ma'aikatan jinya da masu aikin sa kai da kuma wadanda suke aiki a unguwannin birnin, da ba a san daidai yawansu ba, suka fito don sauke nauyin dake wuyansu na yaki da annobar. Yanzu ga wasu labaru game da yadda matasan Wuhan 4 suka yi kokarin dakile annobar COVID-19.

Labaru game da yadda matasan Wuhan 4 suka yi kokarin dakile annobar COVID-19

Yang Xiao, mai shekaru 32 da haihuwa, likita ce dake aiki a sashen ICU na asibitin Zhongnan dake karkashin jami'ar Wuhan. Bayan bullar annobar COVID-19 a Wuhan, nan da nan ta ajiye yaronta a wajen iyayenta, inda ta zauna ta yi aikin ceton wadanda suka kamu da cutar a asibitinsu. Yang Xiao ta ce, ta kara niyyar kokarin zama kwararriyar likita sabo da ta samu amincewa sosai daga wajen marasa lafiya. Yang Xiao tana mai cewa, "Ina son zama kwararriyar likita. Ba na son hawa wani muhimmin mukami, amma dole ne in iya samun mutane marasa lafiya wadanda za su amince da ni sosai. A gabansu, zan iya cewa, 'na iya, ba matsala' saboda kwarewata."

Labaru game da yadda matasan Wuhan 4 suka yi kokarin dakile annobar COVID-19

Wu Xuan, nas ce wadda aka haife ta a shekarun 1990, kuma ta shafe shekaru 10 tana aikin nas a sashen kulawa da yara marasa lafiya a asibiti na uku na birnin Wuhan. Bayan annobar ta bulla a birnin, ta gabatar da takardar neman izinin zuwa asibitin Jin Yintan, inda ake yaki da annoba mafi kamari a birnin. A asibitin Jin Yintan, ita da abokan aikinta sun kula da mutane marasa lafiya wajen 50 wadanda suka kamu da annobar kowace rana. A kullum su kan sha aiki, har ta kan yi aiki na tsawon sa'o'i sama da goma. Wata rana, da ta gaji ainun, abokan aikinta ne suka dauke ta domin fitar da ita daga dakin kwanan marasa lafiya.

Wu Xuan ta ce, ta samu goyon baya da kwarin gwiwa daga wajen iyalinta da iyayenta. Sabo da haka ba ta damu ko kadan ba.

"Mahaifina tsohon soja ne. Ya kan gaya min cewa, a lokacin da yake rundunar soja, idan an ba su wani aiki, dole ne sojoji su yi kokarin shawo kan matsalolin dake gabansu domin kammala aikin da aka dora musu. Kuma tilas ne soja ya sauke nauyin da aka dora masa. Sabo da haka, iyalina da iyayena dukkansu sun tsaya mini. Shugaban asibitinmu ma ya min alkawarin cewa, idan na samu matsala a lokacin da nake aiki, tabbas za su yi kokarin warware ta. Ni ma ina son ba da gudummawata. Yanzu na cika alkawarina, ina farin ciki sosai."

Labaru game da yadda matasan Wuhan 4 suka yi kokarin dakile annobar COVID-19

Peng Jing, wadda aka haife ta a shekarar 1986, sakatariyar ce a sashen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na wata unguwar mazauna birnin Wuhan, inda ake da magidanta fiye da 4300. A kowace rana, ma'aikata 11 na hukumar dake kulawa da unguwar su kan yi aikin kididdiga da yin rajista da kuma gabatar da wadanda suka kamu da annobar, da sayo wa mazauna wadanda suke zaune a gida kayayyakin masarufi da suke bukata, har ma da rarraba musu kifaye masu rai da kulawa da dabbobin da wadanda suka kamu da cutar suke kiwo. A farkon lokacin bullar annobar, kowace rana, su kan amsa wayoyi har fiye da sau 100, kuma barcin da suke yi ba ya wuce awa 4 ko 5 ba. Bayan da aikin dakile annobar ya zama aiki na yau da kullum, Peng Jing wadda ta yi shekaru 11 tana kwarewa kan aiki a unguwar yanzu tana cike da karin imani kan aikinta.

"A da, ina tsammanin, nauyin da aka dora mana shi ne daidaita wasu harkokin yau da kullum game da mazauna. Ba shi da amfani sosai. Amma, bayan bullar annobar, mun gano cewa, aikinmu yana da muhimmanci matuka. Idan dukkanmu mun sauke nauyin da ke wuyanmu, za a iya hana yaduwar annobar a tsakanin mutane."

Labaru game da yadda matasan Wuhan 4 suka yi kokarin dakile annobar COVID-19

Li Yu, wani saurayi mai shekaru 23 da haihuwa, ya bude wani shagon sayar da shayi mai madara a watan Nuwamban bara, yawan kudin da ya samu ba shi da yawa. Amma a cikin lokacin yaki da cutar, wannan saurayi ya sa niyyar samar da shayi mai madara kyauta ga dukkan ma'aikatan jinya da matasan da suke aikin kai sakonni cikin sauri da masu aikin sa kai a unguwannin mazauna.

"Ni dan birnin Wuhan ne, a shafin sada zumunta, na ga mutane da yawa suna kokarin bayar da gudummawarsu wajen dakile annobar. Sabo da haka, a matsayin dan Wuhan, dole ne in ba da gudummawata gwargwadon karfina. Na bayar da wannan gudummawar ne bisa tunani na 'kauna'."

Jama'a masu sauraro, a lokacin da wadannan matasa suke yawo a titunan birnin Wuhan, dukkansu matasa ne na yau da kullum, amma a lokacin da ake dakile annobar, dukkansu sun zama jarumai, suna kokarin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kamar yadda ake fatan matasa su yi wajen bunkasa kasar Sin. (Sanusi Chen)