logo

HAUSA

Mai tsara fasalin kayan sawa dan asalin Kenya yana ba da kayan rufe baki da hanci kyauta ga matalauta

2020-04-29 11:51:18 cri

A halin da ake ciki yanzu, bisa bazuwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 cikin sauri a nahiyar Afirka, bi da bi, kasashen Afirka sun fitar da tsauraran manufofi domin hana yaduwarta. Alal misali a kasar Kenya, akwai tara mai yawa ga duk wanda bai sa abun rufe baki da hanci a waje da gida ba. Mai yiwuwa ma a aika da mutum gidan yari har tsawon watanni shida.

Amma ga wasu mutanen dake fama da talauci, akwai wahala su mallaki marufin baki da hancin, saboda ba su da kudin saye. A don haka ne wani mai aikin tsara fasalin kayan sawa na kasar David Avido, ya samar da kayan rufe baki da hanci masu yawan gaske domin bai wa matalauta kyauta.

David Avido, 'dan asalin kasar Kenya ne wanda ke aikin tsara fasalin kayayyakin tufafi a kasar, kayan da yake tsarawa dai sun taba halartar bikin nune-nunen kayan da aka shirya a birnin Beilin na kasar Jamus, an kuma haife shi ne a unguwar Kibera ta kasar, wadda ta kasance wurin tsugunar da matalauta mafi girma na biyu a nahiyar Afirka. A bana kuwa yana da shekarun 24 da haihuwa ne kacal.

Bayan bazuwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a Kenya, unguwar tsugunar da matalauta, inda tsarin kiwon lafiyarta ba shi da inganci na matukar jawo hankalin jama'a. A unguwar Kibera, mai fadin muraba'in kilomita 2.5 kacal, an tsugunar da mutane kusan miliyan daya, wadanda ke zaman rayuwa a cikin gidajen kwanan da aka gina da karfe, babu ruwan famfo, babu gine-ginen fitar da ruwa.

Avido ya bayyana cewa, mutanen dake zama a cikin unguwar ba su da kudin sayen kayan rufe baki da hanci, a don haka yana ganin cewa, ya dace ya samar musu tallafi gwargwadon karfinsa, yana mai cewa, "Dalilin da ya sa na tsai da kudurin samar da kayan rufe baki da hanci shi ne, ni kaina na taba shan wahala, mutane da yawa suna zaman rayuwa tare a dan karamin wuri, idan wani ya kamu da cutar, cikin sauri zai yada kwayar ta ga sauran mutane. Kana na san kudin shigar mutanen wurin kadan ne kwarai, ko wace rana ba sa samun abun da ya kai shilling na Kenya 300 ko 400, kwatankwacin dala 4 kacal. Shi ya sa na tsai da kudurin samar da kayan rufe baki da hanci domin ba su kyauta, saboda ba su da kudin saye da kan su."

Duk da cewa, Avido yana aikin tsara fasalin tufafi ne, amma bai taba tsara fasalin abun rufe baki da hanci ba, shi ya sa ya tambayi likitoci da mutanen da abun ya shafa, a karshe dai ya fara samar da kayan da zaren Ankara, wani irin zare na gargajiyar Afirka, kana irin wannan zare yana da launi mai haske, wanda ya fi samun karbuwa daga mutanen unguwar Kibera. Avido ya samar da kayan rufe baki da hanci ne da zare guda biyu, ana iya sa zaren maganin kwayar cuta ko takarda a ciki, kuma ana iya sake yin amfani da shi, bayan an tsabtace shi.

Avido ya gaya mana cewa, duk da cewa, mai yiwuwa kayan rufe baki da hanci da ya samar ba za su iya hana bazuwar kwayar cutar COVID-19 kai tsaye ba, amma za su taka rawa wajen rage cudanyar fuskokin jama'a. Ya ce, kayan rufe baki da hanci da ya samar, sun samu karbuwa matuka daga wajen mazauna unguwar Kibera, saboda yana da kyan gani, a cewarsa: "Na je na tambayi likitoci da mutanen da abun ya shafa da dama, domin kara kyautata ingancin kayan rufe baki da hancin. Duk da cewa, kayan da na samar ba za su iya hana bazuwar kwayar cutar COVID-19 daga duk fannoni ba, amma ko shakka babu za su taimaka."

Hakika Avido shi kansa yana fama da wahala, saboda ba shi da isasshen kudin sayen zaren da yake bukata, amma ya riga ya samar da kayan da yawansu ya kai sama da 7200.

Avido ya girma ne a unguwar Kibera, shi ya sa ya fahimci unguwar matuka, ya taba bayyana cewa, yayin da yake tsara tufafi, kullum yana tunanin iska da teku da tituna. Ya ce, yana son canja tunanin sauran mutane, wadanda ke ganin wani abu mai daraja ba zai iya samo asali daga matalauta ba. Yana son gaya wa al'ummun kasashen duniya cewa, ya kan tsara tufafi ne bisa tushen zaman rayuwarsa, a unguwar tsugunar da matalauta.

Ban da samar da kayan rufe baki da hanci kyauta ga mutanen dake zaman rayuwa a unguwar Kibera, Avido yana kuma yayata muhimmancin kiyaye nisa tsakanin mutane, da wanke hannu yayin da ake kokarin dakile annobar COVID-19, kana ya jaddada cewa, yanzu abu mafi muhimmanci shi ne hada kai, yana mai cewa, "Hada kai zai kara karfinmu, kamar yadda ake bukatar taimako, su ma suna bukatar goyon bayan sauran mutane, shi ya sa nake kokarin samar da kayan rufe baki da hanci domin baiwa mutane kyauta."(Jamila)