logo

HAUSA

Jami'in WFP: ra'ayin kariya zai tsananta matsalar rashin abinci

2020-04-23 13:28:54 cri

Rahoton da hukumar shirin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya wato WFP ta fitar ya nuna cewa, ganin yadda annobar COVID-19 ke kara illata tattalin arzikin duniya, adadin mutanen da za su fuskanci babbar matsalar karancin abinci zai karu zuwa miliyan 265 a duk fadin duniya. Wani jami'in hukumar WFP ya ce, ra'ayin samar da kariya zai tsananta matsalar.

Rahoton baya-bayan nan da hukumar WFP ta fitar ya bayyana cewa, daga cikin mutane miliyan 135 dake fuskantar matsalar rashin abinci, akwai miliyan 73 a nahiyar Afirka. Kuma alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun shaida cewa, an samu barkewar fadace-fadace sama da dubu 20 a bara a Afirka, abun da ya tilasta jama'a suka bar muhallansu, da kawo tsaiko ga ayyukan noma da samar da abinci. Har wa yau, wasu iftila'i ciki har da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa da fari sun sa mutane akalla miliyan 33 cikin matsalar rashin abinci, ga kuma matsalar farin dango dake addabar gabashin Afirka ta jefa miliyoyin al'umma cikin hadari.

Jami'in hukumar WFP mai kula da harkokin gaggawa da shawo kan matsala, Matthew Mcilvenna ya ce:

"Daya daga cikin muhimman dalilan da suka jawo matsalar yunwa a nahiyar Afirka, musamman gabashin nahiyar, shi ne tashe-tashen hankali da suka ki ci suka ki cinyewa wadanda suka tilasta jama'a suka bar matsugunansu. Wadannan mutane sun rasa abun dogaro kana suna bukatar taimako. A yankin kahon Afirka dake gabashin nahiyar, akwai makaurata sama da miliyan 6 da 'yan gudun hijira fiye da miliyan 3. Haka kuma akwai sauran wasu miliyoyin al'umma wadanda suke jin radadi sakamakon bala'un ambaliyar ruwa ko fari."

Sakamakon illar da annobar COVID-19 ke haifarwa, ana kara samun mutanen da suka rasa ayyukan yi a Afirka, kuma matsalar rashin abinci na ci gaba da tsananta. Matthew Mcilvenna ya ce, dakatar da zuwa makarantu ya sa aka daina samar da tallafin abinci ga yara, matsalar da ta shafi yara sama da miliyan 4 a Afirka. Dadin dadawa, an samu hauhawar farashin abinci a wasu sassan nahiyar, abun da ya kawo babbar matsala ga mutanen da ba su iya samun albashi mai tsoka ba.

Matthew Mcilvenna ya kara da cewa:

"Abun da ya fi muhimmanci yanzu shi ne ci gaba da tallafawa wadannan mutane. Muna bukatar kokarin rarraba abinci a wuraren da suka taru, saboda rigakafi ya fi magani. Idan annobar COVID-19 ta ci gaba da illata harkokin samar da abinci, babu bukatar damuwa."

Mista Mcilvenna ya jaddada cewa, yaduwar annobar COVID-19 tana haifar da kalubale ga gwamnatocin kasashe daban-daban daga dukkan fannoni, wato daga bangaren lafiyar al'umma, zuwa kawar da talauci da samar da guraban ayyukan yi da isasshen abinci. Duk da cewa kasashe daban-daban a Afirka sun rufe iyakokinsu, amma suna ci gaba da karfafa hadin-gwiwa domin tabbatar da musanyar manyan hajoji tsakaninsu. Mcilvenna ya ce, ra'ayin samar da kariya zai haifar da mummunan tasiri ga matsalar karancin abinci, inda ya ce:

"Muna ganin cewa gwamnatocin kasashe daban-daban na takaita zirga-zirga, musamman zirga-zirga tsakanin al'umma, amma ban da musanyar abinci da amfanin gona. A sabili da haka, ya kamata mu tabbatar da cewa ana musanyar wadannan hajoji tsakanin kasa da kasa, kana mutanen da suke da bukata za su iya sayen abinci bisa farashin da ya dace. Amma idan mun ci gaba da rike ra'ayin samar da kariya domin tinkarar rikicin, halin zai ci gaba da tabarbarewa."(Murtala Zhang)