logo

HAUSA

Hakikanin Yan Afrika A Guangzhou

2020-04-13 13:09:52 cri

Hakikanin Yan Afrika A Guangzhou

 

Wani dan kabilar Igbo dake harkokin kasuwanci a Guangzhou ya bayyana ra'ayinsa game da abin da ke faruwa a Guangzhou na kasar Sin.

A cewarsa, dan uwana, ba wani babban al'amari ba ne ya faru. Ba na bukatar na tambaye ka game da abin da ka riga ka ji saboda kusan mutane 20 sun tambaye ni game da wannan. Dukkan abokan huldar kasuwancina, da abokaina dukkansu sun yi mini wannan tambaya, don haka na san kana son tambaya ni ne game da yadda ake korar bakaken fata daga gidajensu da kuma otel-otel.

Ka san yadda mutane suke. Da zarar sun ji labarai, sai su kara nasu a cikinsa, sai su kara masa wasu abubuwa domin ya kara yin kyau. Na dawo gida daga wajen aiki sai na shiga shawa domin na yi wanka. To game da batun bidiyo wanda ku kalla, labaran da kuka ji game da Guangzhou.

Tun gabanin a rufe bodoji kuma a dakatar da harkokin sufurin jiragen sama daga shigi da fici, wasu mutanenmu suna zuwa su sayi kayayyaki. Jami'ai Sinawa sun fada musu su killace kansu. Hakan ya sa suka dauke su zuwa otel saboda sun fadawa dukkan otel kada su karbi baki 'yan kasashen waje. Jami'an su ne ke gudanar da aikin karbar baki, sun fitar da kai, kuma sun kai ka otel. Za su dinga duba ka a kowace safiya, za su dinga gwada yanayin zafin jikinka domin su tabbatar ko kana da wasu alamun kamuwa da cutar ko a'a. Bayan kwanaki 14 za su fitar da kai daga nan za ka iya ci gaba da harkokin kasuwancin ka.

Amma kwanaki 3 zuwa 4 gabanin cikar wa'adin kwanakin 14, sai suka gano wasu mutanenmu 3 suna da alamomin kamuwa da cutar. Sannu a hankali, sai suka gano biyu daga cikin mutanen 3 suna da zazzabin maleriya ne ko kuma zazzabin typhoid ko kuma wani abu na daban, amma mutum gudan daga cikinsu yana da cutar COVID-19. Jami'an suna kokarin kulawa da mutumin da ya kamu da cutar, amma sai ya ki yarda ya ce suna son yi masa allura ne domin saka masa kwayoyin cutar don su hallaka shi. Amma sun fada masa cewa lamarin ba haka yake ba, suna son kula da lafiyarsa ne kamar yadda suke kulawa da mutanensu, amma sai ya ki yarda. A maimakon hakan, sai ya yi kokarin yin fada da ma'aikatan lafiyar, amma ni ban sani ba ko sun fada cewar ya burgi wani daga cikinsu a kan girar ido ko kuma a wani waje na daban. Amma ka san yadda yanayin jikin fararen fata yake, idan wani ya dan kurje wani bangare na jikinsa ko kuma idonsa ya yi baki, kuma mazauna yankin suka harzuka game da faruwar hakan yayin da suka ji labarin. Saboda haka, koda shi kansa shugaban 'yan Najeriya mazauna China shi ma ya shiga maganar kuma ya roki mutumin da ya kwantar da hankalinsa domin a kula da lafiyarsa. Sinawa sun fada bayan sun ba shi kulawa cewa, za'a mayar da shi zuwa kasarsa kuma sun amince.

Saboda wannan, sai suka fara bibiyar bakaken fata domin binciken yanayin lafiyarsu. Sai suka ziyarci wuraren da bakaken fata ke cin abinci. Sai suka tarar da wani dan Najeriya mai suna Emma, wanda yake auren wata mata Basiniya. Matar tana dafa abinci inda mutane ke sayen abincin har na tsawon wasu makonni. Sai suka gano cewa wannan matar ta yi tafiya zuwa kauyensu amma ta dawo da cutar. Matar ba ta killace kanta na kwanaki 14 ba amma sai ta fara dafa abincin sayarwa ga mutane. Sannan kuma an gano cewa mafi yawan masu sayen abincin matar bakaken fata ne. Don haka sai jami'an suka rufe dukkan wuraren da bakaken fata ke taruwa da yawa a Guangzhou.

Dukkan wadannan abubuwan sun faru ne a Guangzhou, amma sai mutane suka nuna tamkar lamarin yana faruwa ne a duk fadin kasar Sin. Koda yake, sun rufe dukkan wuraren da bakaken fata ke cin abinci a Guangzhou. Sai suka kafa hujja da cewa bakaken fata ne suke sayen abinci matar, kuma ta jima tana sayar musu abinci a kwanaki masu yawa, bakaken fata da yawa sun dauki cutar daga jikin matar. Saboda haka, sai aka umarci wadannan mutanen da su killace kansu su zauna a cikin gidajensu har zuwa lokacin da za'a warware dukkan al'amurra dake shafar wannan matar da kuma mutanen da ta yi mu'amala da su.

Sai jami'an lafiya suka dinga bi gida gida don yin gwajin yanayin zafin jikin mutane da yi musu binciken lafiya. Idan suka gwada ka, za su fada maka ka jira zuwa sa'o'i 24, kuma bayan sa'o'i 24 idan gwajinka ya nuna ba ka dauke da cutar, to sai su ba ka kati domin ka samu damar fita. Wannan katin da shi ne za ka dinga amfani kana shiga kasuwanni da sauran wurare. Don haka wadannan mutanen aka bukace su da su zauna a cikin gida har zuwa lokacin da za'a kammala yin gwajin ga kowanne mutum daga cikinsu domin ta haka ne za'a gane hakikanin wadanda ke dauke da cutar da kuma wadanda ba su dauke da cutar, amma sai suka ki yarda. Sai suka ce sun riga sun killace kansu na tsawon kwanaki 14, don menene kuma za'a ce musu su zauna a gida. Sai dukkansu suka yi watsi da wannan umarni suka fita waje. To a yanzu kuma an baiwa dukkan otel umarni cewa kada su karbi dukkan baki 'yan kasashen waje in ban da otel kwaya daya. Shi ma wannan otel din guda dayan an ba shi umarni cewa kada ya bar kowane mutum ya fita ko ya shiga ciki. Amma ga yadda halayyar mutanenmu take, sai dukkansu suka taru, suka dinga yin hayaniya sai kuma dukkansu suka fito tare. A lokacin da suka nufi kasuwa, sai aka bukace su da su nuna katinsu saboda an riga an sanar da jami'an tsaron yankin cewa su dinga binciken kowa domin su tantance wadanda aka riga aka yiwa gwajin. Yayin da suka gaza nuna katinsu, sai aka hana su shiga kasuwar, kuma bayan da suka koma otel din, sai jami'an kula da otel din suka hana su shiga ciki saboda umarnin da jami'an 'yan sanda suka ba su. Daga nan sai suka fara yada bayanai cewa an kori 'yan kabilar Igbo daga gidajensu da kuma otel-otel kuma an umarce su da su koma gida. Wannan shi ne labarin a yanzu.

Hakikanin Yan Afrika A Guangzhou

Babu wani abu da ya faru face abin da na riga na fada maka. Mutane sun kalli bidiyon sai suka dinga hayaniya cewa "ku duba yadda ake korar 'yan kabilar Igbo da bakaken fata." Amma an umarce su da su zauna a gida domin a daidaita komai. Suna kokarin warware wannan matsala domin a samu damar shawo kan wannan annobar kafin baiwa mutane damar shiga.

Mu da muke wannan wajen, an killace mu, an gwada mu kuma an ba mu katin hakan ne ma ya ba mu damar zuwa wurare. Amma mutanen da suke son su dinga shiga wurare ba tare da an yi musu gwajin ba, kuma hakan ba zai yi kyau ga mutanen dake zama a wannan wajen ba. Wannan shi ne abin da jami'an ke kokarin daidaitawa, amma mutunenmu sun kasa gane hakan, kuma suna janyo matsaloli sakamakon yin watsi da umarnin, suna fadin cewa wai an hana su shiga ciki.

Kuma ga mutanen da suka bar gidajensu, jami'an suna zuwa wadannan gidajen domin su bincika ko suna zaune a gida idan kuma ba sa gidan sai jami'an su kulle gidajen saboda an fadawa kowa ya zauna a gida domin suna son su duba kowa kuma su gwada kowa. Don haka idan suka zo suka tarar ba ka gida, to ina ka je ke nan? Tun da an umarci kowa ya zauna a gida, kuma idan ka ki yarda, har suka rufe gidanka, sai kuma ka fito kana cewa wai an kore ka daga gidanka.

Lokacin da suka sanar da mu cewa mu zauna a gida, na shafe tsawon wata guda da mako biyu. Ban fita waje ba. A yanzu babu wanda ya kore ni daga gida na, kuma babu wanda ya ce da ni kada na shiga gida na. Ko a lokacin da na koma harkokin kasuwanci na, na yi hakan har tsawon wata guda, kuma sun sake kira na, suka sake ba ni kayan gwaje-gwaje wanda zan dinga yin gwajin da kaina a kullum har tsawon kwanaki 14. Na yi hakan kuma na nuna musu sakamakon.

Idan ka bi doka to komai zai zo maka cikin sauki, amma kana tunanin suna kokarin cutar kai ne. Don haka duk wata magana da wani zai fada game da batun nan ka yi watsi da ita. Saboda akwai labaran karya masu yawa da ake yadawa. (Mai Fassarawa: Ahmad Fagam)