logo

HAUSA

Kasashen Afirka sun yabawa Sin na kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da Afirka don yaki da COVID-19

2020-04-10 14:39:56 cri

A halin yanzu, cutar numfashi ta COVID-19 tana cigaba da yaduwa a nahiyar Afirka. Cututtuka kalubale ne da dukkan dan Adam ke fuskanta. Sin ta dora muhimmanci ga yanayin tinkarar cutar a nahiyar Afirka, da yin kokarin samar da gudummawar yaki da cutar ga kungiyar AU da kasashen Afirka, da kuma shirya taron masana don yi musayar fasahohin yaki da cutar ta yanar gizo. Kana kamfanoni da hukumomi masu zaman kansu na kasar Sin sun bada taimako ga kasashen Afirka. Kasashen Afirka sun yabawa Sin domin ta samu nasarori kan yaki da cutar da kuma samar da gudummawa ga kiyaye tsaron lafiyar dukkan duniya baki daya.

A tsakiyar watan Maris, Sin da kasashen Afirka sun gudanar da taron masana ta bidiyo kan yadda za a dauki matakan yaki da cutar COVID-19 karo na farko, inda jami'ai da masana kimanin 300 daga kasashen Afirka 24, da cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka, da sassan hukumar WHO dake wasu kasashen Afirka suka halarci taron. Masanan Sin sun yi bayani ga wakilan kasashen Afirka a fannonin hana yaduwar cutar, da gaggauta yin nazarin allurar rigakafin cutar, da hana yaduwar cutar ta kan iyakokin kasa da unguwoyi, da kuma bada jinya a asibiti da bada kariya ga kansu.

Shugaban sashen asusun inshorar kiwon lafiya na kasar Tanzania Rafael Malaba ya ce, Sin ta samu nasarori kan yaki da cutar COVID-19, da ta zama misali ga kasashen Afirka a wannan fanni. Ministar kiwon lafiya ta kasar Habasha Lia Tadesse ta yabawa masanan kasar Sin domin musayar kwarewarta suka yi kan yaki da cutar COVID-19 da shirye-shiryensu na yaki da cutar, wadanda suka bada shawarwari ga kasashen Afirka, da biya bukatun kasarta ta Habasha.

An kiyaye yin hadin gwiwa a tsakanin cibiyoyin yaki da cututtuka na Sin da kasashen Afirka. Direktan cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka John Nkengasong ya bayyana cewa, tsarin kiwon lafiya na kasashen Afirka ba shi da karfi sosai. A halin yanzu, ana tinkarar cutar COVID-19 mai tsanani, kuma Sin ta yi hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, da more fasahohi da matakan yaki da cutar. Ayyukan da Sin ta gudanar sun ba mu imani da karfin gwiwa wajen yaki da cutar.

A ranar 6 ga wannan wata, kayayyakin yaki da cutar COVID-19 da Sin ta bayar gudummawa ga kasashen Afirka 18 sun iso kasar Ghana, wadanda suka hada da na'urorin taimakawa numfashi, da abin rufe baki da hanci samfurin N95, da rigunan bada kariya ga likitoci da sauransu. A halin yanzu, Sin ta riga ta samar da gudummawar kayayyakin likitanci da fasahohi ga kasashen Afirka 30 da cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka don taimakawa kasashen Afirka wajen tantance mutanen da suka kamu da cutar da bada jinya gare su.

Kasashen Afirka sun nuna godiya ga kasar Sin domin ta samar da gudummawa gare su. Kungiyar AU ta bayar da sanarwa cewa, wadannan kayayyaki za su inganta karfin kasashen Afirka wajen tinkarar cutar COVID-19. Ministan kiwon lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ya ce, likitoci da nas-nas na kasar Najeriya za su koyi fasahohi daga ma'aikatan lafiyar kasar Sin, don yaki da cutar yadda ya kamata. Ko da yake har yanzu kasar Sin na fuskantar kalubale sakamakon cutar, amma kamfanonin kasar dake Najeriya suna martaba ra'ayin jin kai don biyan bukatun al'umma, inda suka kawo karin kayayyakin aikin jinya daga kasar ta Sin, hakan ya taimaka wajen warware matsalar rashin kayayyakin dalike cutar da Najeriya ke fuskanta.

A kwanakin baya, an gama aikin gyara asibitin Wilkins na kasar Zimbabwe zuwa asibitin bada jinya ga masu kamuwa da cutar COVID-19, wanda kamfanin Sin ya bada taimako wajen gina shi. Bangaren gudanar da aikin ya yi aikin ba rana ba dare, an yi amfani da kwanaki 10 ko fiye kawai wajen gama aikin, hakan ya kyautata yanayin asibitoci da karfin bada jinya. Ministan kula da kiwon lafiya da kananan yara na kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, saurin kasar Sin ya burge shi sosai. Gwamnatin kasar Sin ta gina asibitin musamman a birnin Wuhan a cikin gajeren lokaci, yanzu kasashen Afirka suna daukar irin wannan mataki mai amfani. Ya ce, Sin tana kokarin taimakawa karin kasashen duniya wajen tinkarar cutar, hakan ya bada imani da goyon baya ga kasa da kasa, Sin ta samar da babbar gudummawa ga dukkan duniya wajen cimma nasarar yaki da cutar cikin hanzari.

Sakatariyar gudanarwa ta kungiyar raya kudancin Afirka wato SADC Stergomena Tax ta bayyana cewa, Sin ta samar da gudummawa ga nahiyar Afirka cikin lokaci, wannan ya shaida zumunta kamar 'yan uwa a tsakaninsu. Sin ta dauki alhakin tsaron rayuwar jama'a da lafiyar jama'arta, kana ta dauki alhakinta wajen kiwon lafiyar dukkan duniya baki daya. Ba za a taba mantawa da gudummawar da Sin ta samarwa kasashen Afirka ba. (Zainab)