logo

HAUSA

Babban sakataren Jam'iyyar Kwaminis ta Italiya: Bude birnin Wuhan ya baiwa Italiya fata nagari

2020-04-09 14:39:10 cri

Jiya Laraba da safe 8 ga wata, aka dage haramcin tafiye-tafiye a birnin Wuhan, bayan shafe kwanaki 76 a rufe. Dangane da wannan batu, babban sakataren Jam'iyyar Kwaminis na kasar Italiya Mauro Alboresi ya bayyana cewa, wannan labari ya baiwa kasar Italiya karfin gwiwa da fata nagari. Ya kuma jaddada cewa, ta hanyar karfafa hadin gwiwar kasa da kasa da taimakawa juna ne kadai za a yi nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19, wadda ta kasance abokin gaba na dukkanin bil Adama. 

Kasar Italiya tana daya daga cikin kasashen da suke fi fama da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, ya zuwa ranar 7 ga wata, sama da mutane dubu 130 aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar, har yanzu birane a fadin kasar Italiya na ci gaba da zama a killace. Babban sakataren Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Italiya Mauro Alboresi ya bayyana cewa, bude birnin Wuhan ya nuna cewa, kasar Sin ta dauki managartan matakai wajen dakile yaduwar annobar, ya kuma baiwa sauran kasashen dake yaki da annobar karfin gwiwa da fata nagari. Ya ce, "Abin da ya faru a birnin Wuhan ya nuna mana cewa, dabarun da kasar Sin ta yi amfani da su tun da farko sun yi daidai, kuma ta wadannan dabaru ne kadai za a iya dakile yaduwar annobar yadda ya kamata. Bude birnin Wuhan ta kwantar wa kasar Italiya da ma sauran kasashen da suke fama da cutar numfashi ta COVID-19 hankali. Kuma bisa fasahohin da aka yi amfani da su a birnin Wuhan, muna sa ran samun raguwar masu kamuwa da cutar, ta yadda za a iya bude biranen da aka killace su, da nufin takaita yaduwar cutar."

Haka kuma, ya ce, cutar ta fara bulla ne a kasar Sin, amma daga bisani ta cimma muhimmin sakamako wajen dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, bayan da dukkanin al'ummomin kasar da su hada kansu don yakar cutar. A sa'i daya kuma, kasar Sin ta sanar da fasahohin da ta yi amfani da su ga duniya, kuma sun taimakawa wasu kasashen duniya wajen yaki da cutar. Yana mai cewa, "Kasar Sin ta zama muhimmin abin koyi a wannan fanni, ita ce kasa ta farko da ta sanar da fasahohin yaki da annobar a kan lokaci, ta yadda Italiya da sauran kasashe duniya, za su iya tunkarar wannan matsala yadda ya kamata. Misali, kasar Sin ta gaya mana cewa, dole ne mu dauki dukannin matakan da za su dakatar da yaduwar cutar. Bisa abubuwan da suka faru a birnin Wuhan, za a fahimci cewa, rufe hanyoyin tafiye-tafiye na birnin Wuhan ya zama mataki mai muhimmanci, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa, dukkanin kasashen dake fama da cutar daukar irin wannan mataki, da nufin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19."

Mauro Alboresi ya kuma jaddada cewa, yayin da duniya ke yi da wannan annoba, kasar Sin ta nuna kyakkyawan halinta na yin hadin gwiwa. Ba kawai ta nuna goyon baya ga kasashe da dama ba, har ma ta samar musu taimakon kayayyaki da fasahohi. Ya ce, annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta zama babban kalubale ga lafiyar dukkanin bil Adama, da zaman lafiyar kasa da kasa, don haka ya kamata kasa da kasa su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, da taimaka juna bisa ka'idar makomar bai daya ta daukacin bil Adama, ta yadda za a yi nasarar wannan yaki. ya ce, "Mun fahimci cewa, ta hanyar hadin gwiwa ce kadai za mu magance matsalar cutar numfashi ta COVID-19. Ko shakka babu, abin da ake bukata a wannan lokaci, shi ne hadin gwiwar kasashen duniya da tsarin likitanci na kasa da kasa. Idan har ana son ganin bayan wannan annoba, dole a hada kai don taimakon juna."

Bugu da kari, ya ce, ya amince da shawarwarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin taron kolin shugabannin G20 kan yaki da cutar numfashi ta COVID-19, musamman ma kan batun karfafa hadin gwiwar nazarin kimiyya kan cutar tsakanin kasa da kasa, yana kuma goyon bayan rawar da kungiyoyin kasa da kasa ke takawa, tare da yin kira ga kasashen duniya da su hada kai don jure tasirin cutar kan tattalin arziki. Yana mai cewa, "Na amince da shawarwarin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ina ganin cewa, allurar rigakafi ita ce dabarar da za a yi amfani da ita wajen warware wannan matsala daga tushe, wadda ke bukatar hadin gwiwar masana kimiyya da fasahar kasa da kasa. A sa'i daya kuma, wannan annoba za ta haifar da hasara ga tattalin arzikin duniya, shi ya sa, muna fatan kungiyoyin kasa da kasa da hukumomin gwamnatocin kasashen duniya za su warware wannan matsala cikin hadin gwiwa. Sabo da ba za mu iya cimma nasara ba, in babu hadin gwiwar al'ummomin kasa da kasa, balle mu fuskanci kalubalolin tattalin arziki da zaman takewar al'umma, sanadiyyar wannan annoba." (Maryam)