logo

HAUSA

COVID-19: Mene ne laifi idan kasar Sin ta taimaka?

2020-04-08 11:19:45 cri

A kwanakin baya ne wani mai sharhi kan harkokin kasa da kasa, Lawal Sale Maida, ya rubuta wani sharhi da aka wallafa a kafofin watsa labaran kasar Sin, mai takem "Mene ne laifi idan kasar Sin ta taimaka".

Bayanan marubucin na zuwa ne, bayan da sabani da ra'ayoyi su ka rika yawo a kafafen sada zumunta bayan da ma'aikatar lafiyar tarayyar Najeriya ta sanar da cewa, ana sa ran zuwan wata tawaga mai kunshe da ma'aikatan lafiya 18 daga kasar Sin da ta kunshi likitoci da nas-nas, don taimakawa Najeriya a yakin da take yi da cutar COVID-19.

Baya ga tawagar ma'aikatan lafiyar da ake sa ran zuwan su Najeriya, akwai kuma kayayyakin kariya da na'urorin taimakawa yin numfashi da su ma ake sa ran za su iso kasar daga kasar Sin, a matsayin tallafi da gwamnatin kasar Sin tare da hadin gwiwar Sinawa dake aiki da zama a Najeriya suna baiwa Najeriya.

Sharhin ya kara da cewa, irin wannan karamci ba sabon abu ba ne, a hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Najeriya a duk lokacin da wata matsalar gaggawa ta kunno kai. Amma, tuni wasu bangarori suka fara yiwa wannan al'amari bahaguwar fahimta, tare da yi mata mummunar fassara a kafafen sada zumunta. Najeriya tana daya daga cikin kimanin kasashe 80 da mahukuntan kasar Sin suka zaba, don cin gajiyar taimakon kayayyakin kiwon lafiya wajen yaki da COVID-19 a duniya. Idan ba a manta ba, a baya-bayan nan, hamshakin dan kasuwar nan na kasar Sin, kana shugaban rukunin Alibaba, Jack Ma, shi ma ya baiwa gwamnatin Najeriyar gudummawar kayayyakin lafiya da na kariya, don yaki da cutar COVID-19.

Sharhin ya ce, ita ma kasar Sin, ta samu irin wannan taimako daga wasu kasashen duniya, a lokacin da take yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da ta bulla a birnin Wuhan. A lokaci na gaggawa, kasashe na bukatar na juna. A saboda haka ne ma, a lokacin da cutar Ebola ta barke a shekarar 2014 a wasu sassan nahiyar Afirka, kasar Sin ta kasance kasa ta farko da ta taimakawa kasashen da wannan cuta ta shafa, har zuwa lokacin da aka ga bayan ta. Kayayyakin da kasar ta samar a wancan lokaci, sun hada da masana kiwon lafiya da na kimiyya da kayayyakin kiwon lafiya da ake bukata.

A cewar daya daga cikin ma'aikatan lafiya da suka shiga aikin yaki da cutar Ebola a kasar Saliyo, Lu Hongzhou, muhimmin aikin da masanan kasar Sin suka yi wajen yaki da cutar Ebola a Saliyo, shi ne horas da ma'aikatan lafiyar kasar a kai a kai, da halartar taron masanan hukumar lafiya ta duniya, da ziyartar cibiyoyin kula da masu fama da cutar. Wannan a cewarsa, ya taimaka wajen kafa dokoki da tsare-tsare wajen dakile yaduwar cutar da shirya kayayyakin lafiya don kwantar da masu fama da cutar ko wadanda ake zaton suna dauke da cutar.

Sharhin ya ce, annobar da ta karade duniya, tana bukatar hadin gwiwar kasa da kasa. Ta haka ne za a gaggauta ganin bayan annobar cikin sauki. Hakika, hukumar lafiya ta duniya tana karfafa daukar irin wannan mataki. Don haka, taimakon baya-bayan da kasar Sin ta ke son baiwa Najeriya, ba wani sabon abu ba ne ko wani abin da ya saba doka. Saboda a 'yan kwanakin nan, duniya ta shaidu musayar ma'aikatan kiwon lafiya, da kayayyakin kariya da sauran kayayyaki tsakanin kasashe, a kokarin da ake yi na ganin bayan makiyin da ke barazana ga daukacin bil-Adama.

Sharhin ya bayyana cewa, kafofin watsa labarai suna ta yada rahotanni, a lokacin wannan annoba, kasar Rasha ta aika taimakon kayayyakin lafiya zuwa kasar Serbia, yayin kasashen Cuba Ukraine suka tura likitoci zuwa Italiya, ita kuma Amurka ta tura taimakon kudi ga kasar Ukraine, Hadaddiyar daular Larabawa kuma ta taimakawa Pakistan da kayayyakin lafiya. Wadannan wani bangare ne na matakan da kasashen duniya suke dauka don taimaka juna a lokacin da bukata ta taso

A don haka, sharhin ya ce, bai kamata a yiwa tayin da kasar Sin ta yi na taimakawa Najeriya bahaguwar fassara ba. Duniya tamkar kauye guda ne kuma bai kamata su rika fadan kalaman da ba su dace ba. A zahiri ma, a wannan lokaci Najeriya tana bukatar kasar Sin fiye da ko wane lokaci, saboda yadda take raba kwarewa da fashohinta ga sauran kasashe.

Duniya baki daya ta kalli irin kunci da aka shiga da ma rayukan da suka salwanta, lokacin da cutar COVID-19 ta bulla a kasar Sin. Haka kuma, duniya ta kalli irin namijin kokarin da gwamnati da al'ummar Sinawa baki suka yi, wajen ganin bayan wannan cuta. Wannan ne ma ya sa, yanzu haka, kasar Sin ta ke mayar da hankali wajen taimakawa sauran kasashen duniya dake fama da wannan annoba, da kayayyaki da ma'aikatan lafiya don yakar wannan annoba.

A sakamakon yadda wasu 'yan Najeriya suka yiwa wannan batu bahaguwar fassara ne, ya sa babban darektan hukumar fadakar da jama'a ta Najeriya Garba Abari, ya yi karin haske don wayar da kan 'yan kasar kan wai "Najeriya za ta shigo da likitocin kasar Sin don su karbi aikin yaki da CIVID-10". Ya ce, likitocin kasar Sin, za su zo Najeriya ne, don raba fasahohin da kasar ta yi amfani da su wajen yaki da COVID-19 da likitocin kasar ta Najeriya.

Shi ma shugaban kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar wakilan Najeriya, Yusuf Buba Yakub, ya yi kira ga 'yan Najeriya cikin wata sanarwa, da su yi la'akari da alakar dake tsakanin Najeriya da sauran kasashen duniya, ciki har da yarjeniyoyin kasa da kasa da dokoki da suka shafi kasar Najeriya da sauran kasashen duniya.

Shugaban ya kuma yi Allah wadai da bayanai marasa tushe da wasu ke bazawa kan wannan batu.

Ya ce, taimakon da kasar Sin ta yi niyar baiwa Najeriya, babbar gudummawa ce, kuma munanan kalaman da wasu ke yadawa, babu abin da za su haifar, sai zaman dar-dar kawai tsakanin 'yan Najeriya. Kasar Sin ta yi haka ne da kyakkyawar manufa. (Ibrahim)