logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi bayani kan yadda ta fitar da bayanai game da COVID-19 da bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin kandagarki da hana yaduwar annobar

2020-04-07 13:39:21 cri

Tun lokacin da cutar numfashi ta COVID-19 ta barke, a kowane lokaci kasar Sin tana martaba tsarin al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama, ba tare da rufa-rufa ba, da nuna adalci da sauke nauyi, da samar da bayanai a kan lokaci, da raba fasahohin kandagarki da hana yaduwar cutar da jinyar masu fama da cutar da hukumar lafiya ta duniya da kasa da kasa, da karfafa alaka a fannin yin binciken kimiya, da kokarin taimakawa dukkan bangaori, duk wadannan matakai, sun samu yabo da ma amincewa daga al'ummomin kasashen duniya.

Karshen watan Disamban shekarar 2019

Cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta birnin Wuhan dake lardin Hubei na kasar Sin, ta gano masu fama da cutar numfashi da ba a san musabbabin ta ba.

Ranar 3 ga watan Janairun shekarar 2020

Tun daga wannan rana, a kowane lokaci, kasar Sin ta ke sanar da WHO, da kasashe da kungiyoyin shiyya shiyya da abin ya shafa da ma yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin kan bayanan annobar.

Haka kuma, kasar Sin ta fara sanar da kasar Amurka a kai-a kai bayanan da suka shafi yanayin cutar da ma matakan kandagarki da hana yaduwar annobar ta COVID-19

Ranar 4 ga watan Janairu

Jami'in dake kula da cibiyar hana yaduwar cututtuka(CDC) da takwaransa na Amurka, sun tattauna ta wayar tarho kan yanayin annobar. Dukkan sassan biyu, sun amince su rika tuntubar juna kan yadda za su rika yin hadin gwiwa game da bayanai da fasahohi.

Ranar 5 ga watan Janairu

Kasar Sin ta sanar da hukumar lafiya ta duniya(WHO) game da yanayin annobar. A karon farko, WHO ta ba da rahoton wadanda suka kamu da cutar numfashi da ba a san abin da ke haddasa ta ba a Wuhan na kasar Sin.

Ranar 7 ga watan Janairu

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar Sin CDC, ta yi nasarar gano yanayin kwayar halittar cutar.

Ranar 8 ga watan Janairu

Shugabannin cibiyoyin hana yaduwar cututtuka na kasashen Sin da Amurka, sun tattauna ta wayar tarho, don tattauna yadda za su yi musayar tsare-tsare da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Ranar 9 ga watan Janairu

Wata tawagar masana ta hukumar lafiya ta kasar Sin ta samar da bayanan kwayoyin cutar numfashi da ba a san abin da ya haddasa ta ba a Wuhan. Kasar Sin ta sanar da WHO game da yanayin annobar da ma irin ci gaba da ta samu wajen gano yanayin kwayoyin halittar cutar.

Ranar 12 ga watan Janairu

Hukumar lafiya ta birnin Wuhan ta gyara sunan cutar daga " Cutar numfashi da ba a san abin da ya haddasa ta ba" zuwa "cutar numfashi a sanadin kwayar cutar Novel Coronavirus".

Kasar Sin ta mika bayanan yanayin kwayar halittar cutar ga Hukumar lafiya ta duniya, an kuma adana su a rumbun musayar bayanan ciwon marisuwa na duniya(GISAID) tare kuma da raba shi ga kasashen duniya.

Ranar 19 ga watan Junairu

cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Amurka ta tuntubi takwararta ta kasar Sin, kan halin da ake ciki dangane da matakan kariya da dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Ranar 21 ga watan Junairu

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar a shafinta na website cewa, ta tura tawagarta zuwa birnin Wuhan na kasar Sin daga ranar 20 zuwa 21 ga watan.

Hedkwatar cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta Wuhan, ta fitar da sanarwa ta farko a ranar 23 ga watan na Junairu, daga nan ne kuma aka rufe filin jirgin sama da tasoshin jirgin kasa na wucin gadi, daga karfe 10 na safiyar ranar. Ma'aikatar sufuri kuma ta fitar da wata sanarwa cikin gaggawa, inda ta sanar da dakatar da harkar zirga- zirgar ababen hawan fasinja a kan tituna da yankunan ruwa na Wuhan.

Ranar 25 ga watan Junairu

Cibiyar CDC ta kasar Sin da asibitoci da cibiyoyin bincike daban daban suka wallafa wani bayani mai taken "sabuwar kwayar cutar Corona, Basine mai limonia a shekarar 2019". An gano cewa, a samu wani sabon nau'in kwayar cutar dangin Corona da ba a taba ganin irinta ba a baya. Wadda ta zama ta 7 a dangin kwayar cutar Corona da kan kama bil adama.

Ranar 27 ga watan Junairu

Daraktan hukumar lafiya ta kasar Sin Ma Xiaowi ya tattauna da Aza, sakataren ma'aikatar kula da lafiya da hidimtawa al'umma ta Amurka, domin musayar bayanai kan halin da ake ciki dangane da matakan kariya da na takaita yaduwar sabuwar kwayar cutar.

Ranar 28 ga watan Junairu

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da daraktan hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a birnin Beijing.

Ranar 30 ga watan Junairu

Hukumar lafiya ta kasar Sin ta sanar da Amurka a hukumance cewa, ana maraba da ta shiga cikin ayarin kwararru na hadin gwiwa na hukumar WHO. Inda Amurka ta aiko da sakon godiya a wannan rana.

Zuwa karshen ranar 3 ga watan Fabreru

Kasar Sin ta sanar da Amurka bayanan kandagarki da na dakile yaduwar annobar har sau 30. Bayanan sun kunshi tsarukan duba marasa lafiya da jinyarsu da na kariya da dakile yaduwar cutar da kuma huldar kasar Sin da sauran sassan duniya kan fasahohin kariya da matakan dakile cutar, wanda ya gudana karkashin shugaban aikin na cibiyar CDC ta kasar Sin.

Ranar 4 ga watan Fabreru

Shugaban CDC ya tuntubi daraktan cibiyar kula da borin jini da cututtuka masu yaduwa domin musayar bayanai kan yanayin annobar.

Ranar 7 ga watan Fabreru

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na Amurka Donald Trump ta wayar tarho bisa gayyatar da aka yi masa.

Ranar 8 ga watan Fabreru

Shugabannin sassan lafiya na kasar Sin da na Amurka suka kara tattaunawa kan yadda za a shirya shigar kwararrun Amurka cikin tawagar kwararru na hadin gwiwa na WHO dake nazarin cutar.

Ranar 11 ga watan Fabreru

Kwararru daga cibiyar CDC ta kasar Sin sun yi taro ta waya da takwarorinsu na sashen yaki da murar influenza na cibiyar CDC ta Amurka, domin tattaunawa da musayar bayanai kan dakile yaduwar annobar.

Ranar 12 ga watan Fabreru

Ma'aikatar lafiya ta Amurka ta aike da wasika ga shugaban hukumar lafiya ta kasar Sin, domin bangarorin biyu su tattauna kan batun kiwon lafiya da hadin gwiwa kan ayyukan kariya da na dakile annobar da sauran wasu shirye-shirye.

Ranar 14 ga watan Fabrairu

Shugaban hukumar raya tattalin arzikin gwamnatin kasar Amurka Lawrence Kudlow ya ce, kasar Sin ta boye wasu abubuwa game da yaki da cutar numfashi ta COVID-19. Dangane da wannan batu, mai kula da harkokin gaggawa na hukumar lafiyar duniya ta WHO Michael Ryan ya bayyana cewa, tsokacin da Lawrence Kudlow ya yi ba gaskiya ba ne, gwmnatin kasar Sin tana yin hadin gwiwa da hukumar WHO yadda ya kamata, kuma ba tare da boye kome ba.

Ranar 16 ga watan Fabrairu

Tawagar masanan Sin da WHO sun fara aikin bincike na kwanaki 9 a kasar Sin, cikin wadannan kwanaki 9, sun ziyarci biranen Beijing, Chengdu, Guangzhou, Shenzhen da kuma Wuhan da sauransu.

Ranar 18 ga watan Fabrairu

Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta amsa wasikar da ma'aikatar lafiya da samar da hidima ga al'ummar kasar Amurka ta aika mata, inda bangarorin biyu suka yi shawarwari kan yadda za su yi hadin gwiwar kiwon lafiya da yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Ranar 19 ga watan Fabrairu

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da shugaban Asusun Bill Gates ya aika masa, inda ya nuna godiya ga Gates da asusunsa dangane da goyon baya da suka nunawa kasar Sin wajen yin kandagarki da hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, ya kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su karfafa hadin gwiwa domin yaki da annobar.

Ranar 24 ga watan Fabrairu

Tawagar masanan Sin da WHO ta kira taron manema labarai a birnin Beijing, inda ta nuna amincewa kan kwararan matakan da kasar Sin ta dauka wajen dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, ta ce, Sin ta sami sakamako mai kyau wajen dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, musamman ma a tsakanin mutum da mutum, lamarin da ya sa, ta kare ko a kalla ta jinkirta mutane a kalla dubu dari daga kamuwa da cutar COVID-19.

Ranar 28 ga watan Fabrairu

Tawagar Zhong Nanshan, kwararren masanin ilmin jinya na kasar Sin da wasu asibitoci gami da wasu hukumomin nazari sun gabatar da rahoto mai taken "yanayin kwayar halittar cutar numfashi ta COVID-19 " a mujallar ilmin likitanci ta New England, wato NEJM ta kasar Amurka, inda suka yi bayani kan yadda suka ba da jinya ga mutane 1099, wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19.

Ranar 11 ga watan Maris

Tawagar nazari ta cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Sin CDC ta fidda rahoto mai taken "binciken SARS-CoV-2 da aka yi kan samfuran masu cutar daban daban" a mujallar kungiyar ilmin likitanci ta kasar Amurka, inda karo na farko, aka gabatar da jerin canje-canjen kwayoyin halittar mutanen dake dauke da cutar numfashi ta COVID-19.

Ran 12 ga watan Maris

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga waya ga babban magatakardan MDD António Guterres bisa gayyatar da aka yi masa. A cikin tattaunawar, Xi ya jaddada cewa, Sin na fatan raba fasahohi da dabarunta ga sauran kasashe don yakar COVID 19, da kuma hadin kan kasa da kasa wajen kirkiro magunguna da allurar rigakafi, ita kuma tana taimakawa sauran kasashe da cutar ta dabaibaye gwargwadon karfinta.

Rukunin masanan kasar Sin masu yakar cutar na farko na kasar Sin ya isa Italiya, tare da samarwa kasar kayayyakin tallafi.

Ran 17 ga watan Maris

Sin ta samarwa kasashe 11 na'urorin gwada kwayar cutar COVID 19 kirar kasar Sin nau'o'i 14.

Ran 26 ga watan Maris

Shugaba Xi Jinping ya halarci taron koli na G20 kan yakar COVID 19 tare da ba da jawabi mai taken "Hadin kai don yakar COVID 19 tare".

Alkaluman da hukumar hadin kan kasa da kasa ta kasar Sin ta gabatar na nuna cewa, ya zuwa wannan rana, Sin ta riga ta baiwa kasashe 89 da kuma kungiyoyin kasa da kasa 4 kayayyakin tallafi har sau 4, yanzu kuma, ana shirin samar da taimako na biyar.

Ran 27 ga watan Maris

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na Amurka Donald Trump ta wayar tarho bisa gayyatar da aka yi masa.

Ran 29 ga watan Maris

An ba da sanarwa a taron manema labarai kan tsarin hadin kan bangarori daban-daban wajen yaki da kandagarkin COVID 19 na majalisar gudanarwa ta kasar Sin cewa, Sin ta cimma nasarar hana yaduwar cutar a yankinta.

Ran 30 ga watan Maris

Bisa gayyatar da kungiyar ma'aikatan jinya a fannin numfashi ta kasar Amurka ta yi musu, ma'aikatan jiyya na kasar Sin da takwarorinsu na Amurka sun hau wani dandali kan Intanet na yakar COVID 19, don gabatar da fasahohi da kuma dabarun kasar Sin.

Darektan hukumar lafiya ta kasar Sin Ma Xiaowei ya tattauna da ministan harkokin kiwon lafiya da ba da hidima ga jama'a na kasar Amurka ta wayar tarho, don tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a ran 27 ga watan Maris a cikin tattaunawarsu ta wayar tarho, tare kuma da bayyana halin da Sin take ciki a matakai daban daban wajen magance cutar, da musanyar ra'ayi kan hadin kansu nan gaba.

Ran 31 ga watan Maris

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta riga ta ba da kayayyakin tallafi ga kasashe 120 da kuma kungiyoyin kasa da kasa 4, wadannan kayayyaki sun hadda da abun rufe baki da hanci na yau da kullum, da kuma abin rufe baki da hanci nau'i na N95, kayan kandagarki, da na'urar gwada kwayar cuta da kuma injin taimakon numfashi da dai sauransu. Ban da wannan kuma, kananan gwamnatocin wurare daban-daban na kasar Sin sun baiwa kasashe fiye da 50 kayayyakin tallafi ta hanyar kawancen birane masu sada zumunci na kasa da kasa. Dadin dadawa, kamfanonin kasar Sin kuma, sun samarwa kasashe da kuma kungiyoyin kasa da kasa fiye da 100 kayayyakin jiyya. (Masu Fassarawa: Ibrahim, Fa'iza, Maryam, Amina)