logo

HAUSA

Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a yayin taron musamman na shugabannin G20

2020-03-27 12:15:30 cri

A jiya Alhamis da dare, a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron musamman na shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 da aka shirya ta kafar bidiyo domin dakile cutar numfashi ta COVID-19, inda ya kuma gabatar da wani muhimmin jawabi mai take "A yi hadin gwiwa wajen dakile annobar, ta yadda za a iya shawo kan mawuyacin halin da ake ciki". A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, a gaban annobar COVID-19 da ta barke ba zato ba tsammani, gwamnati da al'ummar kasar Sin ba su ba da kai ba, a kullum suna dora muhimmanci matuka wajen tsaron rayukan mutane da kuma lafiyarsu. Bisa babbar ka'idar "a dauki matakai masu dacewa bisa ilmin kimiyya a lokacin da ake shawo kan annobar cikin hadin gwiwa". Bugu da kari. Sannan dukkan al'ummar Sinawa sun sa kaimi wajen daukar matakan kandagarki da kuma shiga aikin yaki da cutar. A waje daya, kasar Sin tana fitar da dukkan bayanai game da cutar a fili ga daukacin al'ummarta da kuma duk duniya. Bisa namijin kokarin da ta yi, da kuma wahalar da al'ummar Sinawa suka sha, yanzu, yanayin da kasar Sin ke ciki wajen dakile cutar ya dinga samun kyautatuwa. Ana kuma gaggauta komawa bakin aiki a lokacin da ake kokarin farfado da masana'antun samar da kayayyaki. Amma har yanzu kasar Sin ba ta saki jikinta ba ko kadan. A halin da ake ciki yanzu, annobar na yaduwa cikin sauri a duk fadin duniya, yanzu kasashen duniya na bukatar kwakkwarar niyya da hadin gwiwar dakile annobar, ta yadda za su iya cimma nasarar shawo kan annobar da yanzu daukacin bil Adama ke fuskanta tare. Bisa tunanin bunkasa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, kasar Sin tana ci gaba da samar da taimako ga sauran kasashen duniya gwargwadon karfinta da kuma bayar da gudummawarta wajen ba da tabbaci ga bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya.

Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a yayin taron musamman na shugabannin G20

A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, "A lokacin da kasar Sin take cikin mawuyacin hali mafi tsanani, dimbin mambobin gamayyar kasa da kasa sun samarwa bangaren Sin taimako da goyon baya cikin sahihanci. Za mu ci gaba da tunawa da kuma martaba wannan abokantaka har abada. Annoba mafi tsanani abokiyar gaba ce ga daukacin bil Adama. Yanzu cutar COVID-19 wadda take yaduwa a duk fadin duniya, na kawo barzana ga rayuka da lafiyar mutane, har ma ta zama wani kalubale mai tsanani ga fannin kiwon lafiyar bil Adama ga duniyarmu baki daya."

Sannan a cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarwari 4 bisa jigon taron, wato, da farko dai, a sa niyyar hana yaduwar annobar a duk fadin duniya. Sabo da haka, ya kamata a shirya taron ministocin kiwon lafiya na kasashe mambobin kungiyar G20, sannan a karfafa aikin more bayanai da kuma yin hadin gwiwa wajen nazarin magani da allurar rigakafin barkewar annobar. Kuma dole ne a yi hadin gwiwa wajen taimakawa kasashe marasa arziki wadanda ba su da tsarin kiwon lafiya mai inganci. Shugaba Xi na fatan kungiyar G20 za ta iya bada shawarar samar da taimakon dakile annobar. Xi Jinping yana mai cewa, "Bisa tunanin bunkasa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, bangaren Sin yana son samarwa sauran kasashen duniya matakai masu amfani wajen rigakafi da kuma dakile cutar, tare da yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya wajen nazarin magunguna da alluran rigakafin annobar. Bugu da kari, za mu samar da taimako gwargwadon karfinmu ga wasu kasashe, inda annobar ke barkewa."

Na biyu shi ne, a dauki matakan rigakafi da kuma dakile annobar cikin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. Xi Jinping ya nuna cewa, bangaren Sin ya riga ya budewa duk duniya shafukan intanet, inda za a iya samun ilmi da fasahohin rigakafi da kuma dakile cutar COVID-19. Ya kara da cewa, ya kamata kasashen duniya su yi hadin gwiwa domin hanzarta nazarin magunguna da allurar rigakafin cutar da kuma akwatin binciken cutar. Bugu da kari kuma, ya kamata a tattauna kan yiyuwar kafa tsarin yin mu'amalar harkokin tsaron kiwon lafiyar al'umma na shiyya-shiyya.

Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a yayin taron musamman na shugabannin G20

Dadin dadawa, na uku shi ne, bangaren Sin na nuna goyon baya ga kungiyoyin kasa da kasa da su taka rawar gani kamar yadda ya kamata.

"Bangaren Sin na goyon bayan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO da ta taka rawar ba da jagoranci da tsara manufofin rigakafi da kuma dakile cutar bisa ilmin kimiyya, domin kara yin namijin kokarin hana yaduwar annobar tsakanin kasa da kasa. Ya kamata kungiyar G20 ta karfafa aikin more bayanan rigakafi da kuma dakile cutar, sannan ta fitar da matakai masu amfani wajen dakile cutar baki daya. A lokaci mai dacewa, ya kamata a shirya taron koli na kiwon lafiyar duk duniya. Kasar Sin za ta yi hadin gwiwa da sauran kasashen duniya, wajen nuna goyon baya mai karfi ga kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya."

Na hudu shi ne, kara daidaita manyan manufofin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa. Xi Jinping ya nuna cewa, ya kamata kasa da kasa su yi hadin gwiwa wajen daukar matakan adawa da asarar da aka yi musu domin hana raguwar ci gaban tattalin arzikin duk duniya.

Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a yayin taron musamman na shugabannin G20

Daga karshe dai, Xi Jinping ya karfafa cewa, "A wannan muhimmin lokaci, ya kamata mu fuskanci kalubalen dake gabanmu kai tsaye, mu hanzarta daukar matakan dakile cutar. Ina da imani cewa, muddin muka yi hadin gwiwa da taimakawa juna, tabbas ne za mu cimma nasarar shawo kan cutar, da kuma samun kyakkyawar makoma mai haske ga bil Adama."

Mai Martaba Salman bin Abdulaziz Al Saud, sarkin kasar Saudiyya ne ya shugabanci taron kolin na wannan karo da aka yi ta kafar bidiyo. Shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 da na wasu kasashen da aka gayyata a matsayin baki da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa, kamar na MDD, da asusun bada lamuni na duniya da na bankin duniya sun halarci taron. A yayin taron, an fitar da "Sanarwar taron kolin shugabannin kungiyar G20 kan yadda za a dakile cutar COVID-19". (Sanusi Chen)