logo

HAUSA

WHO: An samu rahoton bullar cutar COVID-19 a kasashe 61

2020-03-03 13:05:31 cri

A jiya Litinin 2 ga wata, babban jami'in hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 1 ga watan Maris din nan, ban da kasar Sin, gaba daya akwai kasashe 61 wadanda suka samu rahoton masu dauke da cutar numfashi ta COVID-19, amma ya sake jaddada cewa, kawo yanzu annobar ba ta yi tsananin yaduwa a fadin duniya ba tukuna, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su ci gaba da mai da hankali kan aikin hana yaduwar annobar, ta yadda za a dakile ta a kan lokaci.

A jiya babban jami'in hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya sanar da cewa, ya zuwa ranar 1 ga wata, ban da kasar Sin, gaba daya akwai kasashe 61, wadanda suka samu rahoton kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19, har adadin su ya kai 8739, a cikinsu, wasu 127 sun rasu a sanadin cutar, kana ya yi nuni da cewa, adadin sabbin mutanen da aka tabbatar da sun kamu da cutar a kasar Sin ya kai 206 a wannan rana, wato ranar 1 ga wata, adadin da shi ne mafi kankanta tun bayan ranar 22 ga watan Janairun da ya gabata, yana mai cewa, "A cikin yini guda da ya gabata, adadin sabbin mutanen da aka tabbatar da sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a sauran kasashen duniya a waje da kasar Sin ya ninka adadin na kasar Sin har sau 9, kasashe wadanda annobar ta fi kamari sun hada da Koriya ta Kudu, da Italiya, da Iran, da kuma Japan. Ko shakka ba bu muna damuwa da yanayin da suke ciki."

An gano cewa, adadin sabbin mutanen da aka tabbatar da sun kamu da cutar a Koriya ta Kudu ya kai kusan rabin adadin da aka tabbatar da sun kamu da cutar a fadin duniya, wato ban da kasar Sin, amma dalilin da ya sa haka shi ne, ana samun karin sabbin mutanen da su kamu da cutar ne yayin taron jama'a sau biyar da aka shirya a kasar, wato annobar ba ta samu yaduwa ne a tsakanin cudanyar jama'a a cikin unguwanni ba, a don haka ana ganin cewa, matakan da kasar ta dauka suna taimakawa a bayyane wajen hana yaduwar ta.

Jami'in ya fayyace cewa, tawagar kwararrun hukumar kiwon lafiya ta duniya ta riga ta sauka a birnin Tehran, fadar mulkin kasar Iran, domin gudanar da hadin kai da hukumomin kiwon lafiyar kasar, tare kuma da yin bincike, da ba da jagorancin fasaha kan aikin dakile annobar a kasar, kana an yi jigilar kayayyakin ba da kariya ga masu aikin jinya, wadanda yawan su ya kai dubu 15, da magungunan tantance cutar wadanda za su iya tantance mutane dubu 100, a cikin jirgin saman da ya dauki kwararrun.

Tedros ya sake bayyana cewa, kawo yanzu WHO tana ganin cewa, annobar COVID-19 ba ta yi tsananin yaduwa a fadin duniya ba tukuna, saboda ana iya gano asalin da ya sa yawancin masu kamuwa da cutar suka harbu da ita, haka kuma ban da kasar Sin, ba a gano cewa, an samu yaduwar cutar tsakanin jama'a a cikin unguwanni ba, yana mai cewa, "Na sake jaddada cewa, idan an samu shaida, WHO za ta sanar da cewa, cutar ta yi tsananin yaduwa a fadin duniya nan take, amma mun gano cewa, daga cikin daukacin masu dauke da cutar da yawan su ya kai 88,913 a fadin duniya, kaso 90 bisa dari suna cikin kasar Sin ne, inda mafi yawan su cikin lardi guda dake kasar ne, kana daga cikin daukacin wadanda suka kamu da cutar wadanda suka kai 8739, kaso 81 bisa dari suna cikin kasashe hudu ne."

Ya kara da cewa, WHO tana fatan kasashen duniya za su kara fahimtar cewa, a halin da ake ciki yanzu, muna da karfin hana yaduwar cutar, kuma matakan da muka dauka suna shafar yaduwar cutar, a cewarsa: "Idan muna fama da matsalar yaduwar cutar mura ko "flu" yanzu, to za mu tarar da cewa, cutar tana yaduwa cikin sauri tsakanin jama'a a cikin unguwanni a fadin duniya, kuma ba zai yiwu a rage, ko hana yaduwar ta ba, amma yanzu an samu nasarar hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, a don haka dole ne daukacin kasashen duniya su mayar da aikin hana yaduwar ta a gaban komai, haka kuma su dauki matakai masu yakini tun da wurwuri, ta yadda za a hana yaduwar cutar a kan lokaci, tare kuma da ceton rayukan jama'a yadda ya kamata."(Jamila)