logo

HAUSA

Hira da Samaila Usman dan Najeriya dake karatu a jami'ar Lanzhou ta kasar Sin

2020-03-01 17:10:23 cri

A yayin da ake himmatuwa wajen dakile yaduwar annboar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin, sashin Hausa na CRI ya ci gaba da zantawa da wasu daliban Najeriya wadanda ke karatu a sassa daban-daban na kasar, domin jin ra'ayoyinsu kan matakan da gwamnatin kasar Sin ke dauka na ganin bayan cutar.

A yau ne, wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da da Samaila Usman, wani dalibi dan jihar Yobe wanda ke karatun digiri na uku a jami'ar Lanzhou dake arewa maso yammacin kasar Sin.

 

Hira da Samaila Usman dan Najeriya dake karatu a jami'ar Lanzhou ta kasar Sin

 

Samaila Usman ya bayyana ra'ayinsa game da managartan matakan da hukumar makarantarsu ke dauka domin kare dalibai daga kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19, inda a cewarsa, ma'aikatan jinyar kasar sun cancanci yabo saboda babbar gudummawar da suka bayar wajen shawo kan wannan cuta.