logo

HAUSA

Barkewar cutar COVID-19 a Sin ba zai canja muhimmin matsayin kasar cikin tsarin samar da kayayyakin kasa da kasa ba

2020-02-28 14:40:55 cri

Cikin taron manema labaran da ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ta kira ta yanar gizo a jiya Alhamis, an ce, a halin yanzu, ba a gano labarin cewa, akwai kamfanoni da masana'antu masu yawa da suka kaura zuwa kasashen waje ba, saboda barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a Sin, kuma bisa hasashen da aka yi, tasirin da yaduwar cutar a kasar Sin ta yi wa tsarin samar da kayayyaki zai zama na gajeren lokaci, lamarin da ba zai canja muhimmin matsayin kasar Sin cikin tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa ba.

Cikin wannan taro, shugaban sashen kula da jarin waje na ma'aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin, Zong Changqing ya bayyana cewa, barkewar cutar numfashi ta COVID-19 ta kawo wasu matsalolin sufuri da karancin ma'aikata da sauransu ga kamfanoni da masana'antun kasar Sin. Don gane da wannan batu, ma'aikatar kasuwanci ta kasar ta dauki wasu matakai domin sa kaimi ga kamfanoni da masana'antu su koma bakin aiki. Ya kara da cewa, za a warware matsalolin da kamfanoni masu jarin waje suke fama da su a lokacin da suke komawa bakin aiki.

"Daga ranar 25 ga wata, gwamnatin birnin Shanghai za ta kashe rabin wata wajen ziyartar hedkwatar kamfanoni masu jarin waje da wasu muhimman kamfanonin ketare guda 720, domin taimaka kai tsaye wajen warware matsalolinsu. A sa'i daya kuma, lardin Guangdong ya fidda shirin "yin mu'amala tsakanin shugaban lardin da kamfanonin ketare kai tsaye" domin karfafa shawarwari kan batutuwan sufuri, ma'aikata, kayayyaki da kayayyakin kandagarki, kuma ya riga ya warware wasu matsalolin da kamfanonin ketare guda 40 suka gabatar masa, har babban kamfanin sarrafa sinadarai na BASF ya fara aiwatar da wasu manyan shirye-shiryensa."

Zong Changqing ya ce, bisa binciken da kungiyar kasuwancin Amurka dake kasar Sin ta yi, an ce, akwai kamfanonin da aka ziyarce su 55% dake ganin cewa, yanzu ba su iya tabbatar da tasirin da yaduwar cutar za ta yi wa tsarin gudanarwar ayyukansu cikin shekaru 3 zuwa 5 masu zuwa ba, sa'an nan, 34% na kamfanoni na ganin cewa, yaduwar cutar ba za ta haifar da tasiri kan tsarin gudanarwar ayyukansu ba.

Haka zalika kuma, bisa wasu bincike da nazarin da aka yi, tattalin arzikin kasar Sin za ta ci gaba da bunkasa, da kuma samun karin jarin waje yadda ya kamata, domin galibin kamfanonin kasashen ketare ba su canja shirye-shiryensu na zuba jari a kasar Sin ba, suna da imani kan karfin kasuwannin kasar Sin.

Bugu da kari, Zong Changqing ya ce, a nan gaba kuma, kasar Sin za ta karfafa ayyukan ba da hidima da goyon bayan kamfanonin ketare, bisa tushen yin kandagarki kan yaduwar cutar, domin samar da yanayin zaman karko ga kamfanonin ketare. Ya ce,

"Za mu tabbatar da komawar wasu muhimman kamfanoni masu jarin waje bakin aiki, da wasu masana'antun dake hadin gwiwa da su. Kuma za mu sa kaimi ga kamfanonin samar da motoci da na'urorin wutar lantarki na jarin waje da su fara ayyukansu tare da kamfanonin Sin dake hadin gwiwa da su. Sa'an nan kuma, za mu taimakawa gwamnatocin wurare daban daban wajen aiwatar da manufofin da suka fidda domin ba da rangwame ga kamfanonin yayin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, ta yadda za a karfafa imanin kamfanonin wajen zuba jari da gudanar da ayyukansu a kasar Sin." (Maryam)