logo

HAUSA

Kamfanonin ketare dake kasar Sin sun dawo bakin aiki

2020-02-26 13:15:49 cri

Kwanakin baya, kamfanonin ketare dake sassan kasar Sin sun dawo bakin aiki sannu a hankali a bisa goyon bayan manufofin da gwamnatin kasar Sin ta fitar, kana wani abin farin ciki shi ne yanzu haka wasu sabbin kamfanonin ketare sun fara gudanar da harkokinsu a kasar ta Sin.

Kamfanin kera na'urorin daidaita wutar lantarki na Samsung na kasar Koriya ta Kudu dake yankin masana'antun birnin Suzhou na lardin Jiangsu na kasar Sin yana samar da kaso 20 bisa 100 na masarrafar adana bayanan kwanfuta da ake bukata a fadin duniya, ya zuwa ranar 20 ga wata, adadin ma'aikatan kamfanin wadanda suka dawo bakin aiki ya riga ya kai kaso 95.1 bisa dari na daukacin ma'aikatan kamfanin, kana saboda kwangilolin da aka daddale suna da dama, ya sa ma'aikatan kamfanin ba su huta ba yayin bikin bazara na gargajiyar kasar Sin, amma wasu kamfanonin dake samar musu kayayyakin da suke bukata ba su fara aiki ba tukuna saboda barkewar annobar numfashi ta COVID-19, lamarin da ya yi tasiri ga aikin kamfanin Samsung, amma daga lokacin da gwamnatin birnin Suzhou da hukumomin da abin ya shafa sun gano matsalar da kamfanin ke fuskanta, nan take su ka taimaka masa domin tabbatar da ganin ya samu kayayyakin da yake bukata ta hanyar yin cudanya da kamfanoni biyu dake birnin Kunshan na lardin, yanzu haka kamfanin Samsung yana gudanar da harkokinsa yadda ya kamata, mataimakin babban manajan kamfanin Li Chengchun ya gaya mana cewa, "Tabbas muna cike da imani kan aikin da gwamnatin kasar Sin ta ke yi da kuma yankin masana'antun birnin, hakika ba ma kawai mu ma'aikatan kasar Sin ba, har ma manajojin kamfanin 'yan kasar Koriya ta Kudu su ma suna cike da imani kan gwamnatin kasar Sin."

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, hukumar kasuwancin lardin Jiangsu ta dauki matakai goma domin taimakawa manyan kamfanonin lardin yayin da suke kokarin dawowa bakin aiki, musamman ma karfafawa 'yan kasuwan ketare gwiwa, ta yadda za su kara zuba jari a lardin.

A sa'i daya kuma, wasu sabbin kamfanonin ketare sun fara gudanar da harkokinsu a lardin na Jiangsu, misali a yankin raya fasahohin zamani na birnin Changzhou, kamfanin cinikayyar kasa da kasa na Schneeberger na kasar Switzerland ya yi rajista kuma ya samu lasisin gudanar da harkokinsa a birnin Changzhou ta Intanet, inda ya kasance kamfanin ketare na farko da ya samu lasisin a birnin tun bayan da dokar zuba jarin waje ta fara aiki a kasar Sin a ranar 1 ga watan Janairun bana.

A halin yanzu, duk da cewa ana yaki da annobar numfashi, amma kamfanonin ketare dake kasar Sin suna cike da imani kan makomarsu a nan gaba, darektan sashen kiyaye muhalli na kamfanin Doosan na Koriya ta Kudu Jiao Wenjia ya bayyana cewa, "Kawo yanzu adadin ma'aikatan kamfaninmu wadanda suka dawo bakin aiki ya riga ya kai kaso 94 bisa dari, dukkan su sun himmatu wajen samar da karin kayayyaki, a don haka mun yi hasashen cewa, adadin kayayyakin da za mu samar a bana zai karu matuka idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata."

Mai taimakawa ministan kasuwancin kasar Sin Ren Hongbin ya bayyana cewa, matakan taimakawa kamfanonin ketare da aka dauka, sun riga sun ba da gudammowa, kuma nan gaba za a taimakawa karin kamfanonin ketare domin su dawo bakin aiki, yana mai cewa, "Nan gaba za mu kara mai da hankali kan manyan kamfanonin ketare dake nan kasar Sin domin su dawo aiki yadda ya kamata, musamman ma kan kamfanonin dake shafar sadarwa da kayayyakin kiwon lafiya da ba da ilmi da al'adu da hada-hadar kudi da sauransu, za mu ci gaba da yin kokarin samar musu da muhalli mai inganci, ta yadda za su kara yin imani kan harkokinsu a kasar Sin."(Jamila)