logo

HAUSA

Muhimmancin yarjejeniyar Paris ga rayuwar bil-Adam

2019-11-14 09:24:23 CRI

A ranar Litinin 5 ga watan Nuwanban shekarar 2019 ne, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompoe, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, kasarsa ta fara shirye-shiryen ficewa daga yarjejeniyar sauyin yanayi da aka cimma a birnin Paris na kasar Faransa a shekarar 2015, wannan batu ya janyo hankulan sassan kasa da kasa matuka, ganin cewa, nasarar wannan yarjejeniya, tana iya shafar ci gaban rayuwar bil Adama baki daya.

Muhimmancin yarjejeniyar Paris ga rayuwar bil-Adam

Majalisar dinkin duniya ce ta dauki nauyin shirya wannan yarjejeniya, a wani mataki na hade kan kasashen duniya waje guda, domin yin aiki tare, wajen daukar matakan rage hayaki mai gurbata muhalli dake haifar da mummunan tasiri ga yanayin muhallin duniya.

Tuni dai Amurka ta bayyana aniyarta ta ficewa daga wannan yarjejeniya nan da shekarar 2020, inda har ma shugaban kasar Dornald Trump ya bayyana cewa, matakin kariya ce ga Amurkawa, duba da irin makudan kudade da kasar za ta ci gaba da kashewa idan har ta ci gaba da kasancewa a cikin wannan yarjejeniya. Manazarta na ganin matakin na Amurka, shi ne mafi muni da gwamnatin za ta aiwatar, wanda zai kwance alkawarin da tsohuwar gwamnatin shugaba Obama ta dauka ga duniya.

Muhimmancin yarjejeniyar Paris ga rayuwar bil-Adam

Masana sun yi kashedin cewa, idan har ba a dauki mataki ba, nan da zuwa shekarar 2050, yawan al'ummun duniya da za su rasa matsugunnin su sakamakon bala'u masu nasaba da sauyin yanayi, zai kai mutum miliyan 143.

Wani babban abun tsoro game da ficewar Amurka daga wannan yarjejeniya, musamman a dai-dai lokacin da sauran kasashen duniya, ciki hadda Sin da Faransa ke hankoron karfafa ta shi ne, mai yiwuwa hakan ya sanyaya gwiwar sauran kasashen duniya, ta yadda za su gaza cika alkawuran da suka dauka na cimma nasarar ta.

Abin jira a gani shi ne, ko aniyar manyan kasashen duniya game da cimma muradun wannan yarjejeniya, zai yi nasara ko sauran kasashen duniya za su iya cike gibin da Amurkar za ta samar?. Haka kuma duniya ba za ta manta da irin gudummawar da sauran kasashen duniya masu dora muhimmanci kan yarjejeniyar ke bayawar ga rayuwar bil Adama a yau, da ma zuriyoyin da za su biyo baya ba! (Ahmed, Ibrahim/Sanusi Chen)