logo

HAUSA

Angola da Cape Verde zasu karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu

2018-02-07 11:35:15 CRI

Angola da Cape Verde dukkanninsu mambobi ne na kasashen dake magana da yaren Portugal wato (CPLP) a takaice, suna shirin daukar matakan karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannoni da dama, kamar yadda ministan harkokin wajen kasarAngola Augusto ya tabbatar da hakan.

Augusto ya bayyana hakan ne a Luanda, bayan wata ganawa tsakanin tawagar wakilan kasashen biyu.

Ya jaddada bukatar dake akwai na sake farfado da kyakkyawar hadin gwiwar hukumomin kasashen biyu, a matsayin hadin gwiwar da za ta farfado da dukkan yarjejeniyoyin da aka cimma, da kuma yarjejeniyoyin fahimtar juna da aka rattaba hannu kansu tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Cape Verde Luis Filipe Tavares, ya jaddada matsayin kasarsa na yin hadin gwiwa da Angola a fannoni da suka hada da harkokin soja da tsaro. (Ahmad Fagam)