in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta janye daga karbar bakuncin kofin kwallon kafa na CECAFA
2018-08-30 10:51:23 cri

Kasar Kenya ta bayyana cewa ba za ta iya karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta kasashe zakarun yankunan gabashi da tsakiyar Afirka ba, wato gasar da hukumar kwallon kafar yankunan ta CECAFA ke shiryawa ba. Kenya ta ce rashin kudade ne zai tilasa mata hakura da wannan lamari.

To dai kuma daukar wannan mataki ya jefa yankin da hukumar ta CECAFA cikin wani yanayi na damuwa, kasancewar saura watanni 3 a fara gudanar da gasar.

Shugaban hukumar kwallon kafar kasar ta Kenya Nick Mwendwa, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua da wannan mataki a ranar Talata. Mwendwa ya ce Kenya ta samu damar karbar bakuncin gasar ne a bara, lokacin da kungiyar Harambee Stars ta kasar ta doke ta Zanzibar a bugun daga kai sai mai tsaron gida. To sai dai kuma sauke wannan nauyi zai gagara saboda larurar karancin kudade.

Kasashen yankin 11 ne dai aka tsara za su buga gasar ta bana. Karkashin jagorancin Kenya da CECAFA za a taka leda a gasar ajin kwararru mafi dadewa a yankin. A wannan karo kasashe da yankuna da suka hada da Zanzibar, da Tanzania, da Uganda, da Rwanda, da Burundi, da Habasha, da Eritrea, da Djibouti, da Sudan da kuma Sudan ta kudu ne ake sa ran za su kece raini.

A bangaren sa, babban sakataren hukumar CECAFA Nicholas Musonye ya bayyana takaicin sa game da matakin da Kenya ta dauka. Jami'in wanda ya yi wannan tsokaci a birnin Nairobi ya ce hakan wani kafar ungulu ni ga wannan gasa. Ya ce a ra'ayin sa akwai masu son ganin bayan hukumar ta hanyar kassara ayyukan ta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China